'Ba dalilin Zaɓenka ba Kenan': Ƴan Najeriya Sun Fusata da Tinubu Ya Je Makka Addu'o'i
- ’Yan Najeriya sun soki shirin Bola Tinubu na zuwa Makka domin gudanar da Umara da yi wa ƙasar addu’a, yayin da ake fama da matsin tattalin arziki
- Wasu ’yan Najeriya sun nuna damuwa kan kuɗin da za a kashe wajen tafiyar, inda suka ce shugaban ƙasa ya kamata ya mayar da hankali kan tattalin arziki da tsaro
- Sai dai wasu sun kare Tinubu, suna mai cewa yana da ’yancin neman taimakon Allah, kuma addu’arsa na iya kawo sauƙi ga ’yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja- ’Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyi mabambanta a shafukan sada zumunta kan shirin Shugaba Bola Tinubu na zuwa Makka da ke domin gudanar da Umara.
Tinubu ya je Saudiyya domin yi wa Najeriya addu’a, inda wasu suka tambayi dalilin tafiyar a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki da rashin tsaro.

Kara karanta wannan
Da gaske Tinubu zai tafi Saudiyya domin neman maganin rashin lafiya? Bayanai sun fito

Source: Twitter
Tinubu ya tafi Umrah a Saudiyya
A cewar sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya wallafa a X, ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya mako mai zuwa bayan kammala ibadar.
Legit Hausa ta samu rahoton cewa fadar shugaban ƙasa ta sanar a ranar Laraba cewa Tinubu zai bar Abuja ranar Alhamis zuwa Saudiyya domin gudanar da ibadar Umara.
Sai dai sanarwar ta jawo martani daban-daban a shafin X, inda wasu suka tambayi ko tafiyar za ta taimaka wajen magance matsalolin ƙasar, yayin da wasu suka kare matakin shugaban ƙasar na neman taimakon Allah.
Martanin yan Najeriya kan tafiyar Tinubu
Yan Najeriya da dama sun yi martani mabambanta game da tafiyar Tinubu zuwa Umrah inda wasu ke yi masa ba'a.
Wani mai amfani da X mai suna @DonAzag ya rubuta cewa:
“Ya taɓa zuwa can domin yin addu’a, amma har yanzu komai yana ƙara lalacewa. Allah ba ya amsa addu’ar masu zunubi.”
Haka kuma, @Olisa37 ya nuna damuwa kan kuɗin da za a kashe wajen tafiyar, yana mai cewa shugaban ƙasar zai iya yin addu’a daga Najeriya ba tare da tafiya ƙasar waje ba.
Ya rubuta cewa:
“Ya kamata waɗannan mutane su ji tsoron Allah kaɗan. Duk waɗannan abubuwan ba za su kai mu ko’ina ba.
"Wannan tafiyar za ta ci sama da naira biliyan ɗaya domin kawai ya je ya yi mana addu’a. Ya zauna a Abuja ya yi addu’ar mana, haba!”

Source: Twitter
Wani mai amfani da shafin mai suna @iamyhummy ya kuma tambayi inda shugaban ƙasar zai nufa bayan kammala ibadar, yana zargin cewa akwai yiwuwar ya wuce Faransa.
Ya rubuta cewa:
“Don Allah ku tambaye shi inda zai wuce bayan ya tashi daga can. Mai yiwuwa Faransa ce.”
A nasa ɓangaren, @djokaymegamixer ya bayyana cewa abin da Najeriya ke buƙata shi ne shugabanci nagari, ba tafiye-tafiyen addini da ake yi domin neman mafita daga matsalolin ƙasa ba.
Ya ce:
“Ba za a iya yaudarar Allah ba. Abin da Najeriya ke buƙata shi ne shugabanci mai ɗaukar nauyi da amsa buƙatun jama’a, ba tafiye-tafiyen nuna addini ba.
“Babu wata ziyara da za a kai ko’ina a duniya da za ta gyara ƙasar da shugabanninta ke gaya wa jama’a su yi azumi yayin da su kuma suke cin moriyar rayuwa."
Wani mai amfani da shafin mai suna @friday_ibezim ya lissafa matsalolin da ƙasar ke fuskanta, inda ya tambayi ko tsarin da shugaban ƙasar ke bi ya dace da halin da talakawa ke ciki.
Ya rubuta cewa:
“Akwai yunwa, sai ya tafi. Akwai rashin tsaro, sai ya tafi. Akwai rashin ingantaccen kiwon lafiya, sai ya tafi. Akwai ƙarancin ababen more rayuwa, sai ya tafi.
“Akwai rashin aikin yi, sai ya tafi. Akwai matsanancin talauci, sai ya tafi.
“Idan manajan kamfaninka yana gudanar da aikinsa haka, za ka ji daɗi? Za ka ci gaba da gode wa Allah kana kallon kamfaninka yana durƙushewa?”
Sai dai ba dukkan ’yan Najeriya ne suka soki shirin tafiyar Tinubu ba, domin wasu sun kare shi, suna masu cewa yana da ’yancin neman taimakon Allah domin ƙasar, cewar Leadership.
Umrah: Atiku ya caccaki Bola Tinubu
Mun kawo muku rahoton cewa Atiku Abubakar ya zargi Bola Tinubu da yiwuwar amfani da tafiyar Umrah a da wata manufa yana mai cewa bayanan sirri sun nuna cewa Faransa ya ke son zuwa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bukaci fadar shugaban ƙasa ta rika fitar da hotuna da bidiyoyi masu dauke da ranar da aka ɗauke su, domin tabbatar da Tinubu yana Makkah.
Asali: Legit.ng

