PRP Ta Yi Kaca Kaca da Shirin Tinubu, Ta Tabo Batun Kisan Sheikh Yahaya Masussuka

PRP Ta Yi Kaca Kaca da Shirin Tinubu, Ta Tabo Batun Kisan Sheikh Yahaya Masussuka

  • Jam’iyyar PRP ta soki shirin Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu, tana zargin gwamnatinsa da gaza magance matsalar rashin tsaro da talauci
  • Shugaban PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce ’yan Najeriya za su ci gaba da neman kariya daga masu garkuwa da mutane da masu kisan kai
  • Jam’iyyar ta kuma yi Allah wadai da kisan Sheikh Yahaya Masussuka a Katsina, tare da kira ga jami’an tsaro su kama waɗanda suka aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar PRP ta soki ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu, tana zargin gwamnatinsa da gaza magance matsalar rashin tsaro da yaɗuwar talauci a ƙasar.

Jam’iyyar ta ce ’yan Najeriya za su ci gaba da neman kariya daga masu garkuwa da mutane da masu kisan kai, duk da cewa jam’iyyar APC ta fara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tafiyar Tinubu zuwa Makkah ta jawo masa abin da bai yi zato ba

Shugaban PRP.
Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed a ofis Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya shugaban PRP na kasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya fitar jiya Alhamis.

Ya bayyana gangamin APC na baya-bayan nan a Kaduna a matsayin wani shiri da aka tsara domin nuna cewa gwamnati na da farin jinin jama’a, duk da abin da ya kira ƙarancin nasarorin da ta samu.

Ya zargi masu shirya gangamin da kashe kuɗaɗen al’umma fiye da kima, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke fama da matsanancin ƙuncin tattalin arziki da rashin tsaro.

PRP ta yi Allah wadai da kisan Masussuka

Baba-Ahmed ya lura cewa yayin da APC ke gudanar da gangaminta, ana zargin ana sace mutane daga gidajensu a cikin birnin Kaduna, yayin da al’ummomin karkara a wasu sassan ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-hare ba kakkautawa.

Ya kuma yi Allah wadai da kisan Sheikh Yahaya Masussuka a gidansa da ke Dutsin-Ma, jihar Katsina, inda ya buƙaci hukumomin tsaro su gaggauta kama waɗanda ke da hannu tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Damuwar PRP kan lafiyar Tinubu

Shugaban PRP ya kuma nuna damuwa kan lafiyar Shugaba Tinubu, inda ya buƙace shi da ya tabbatar ana gudanar da cikakken binciken lafiyarsa da kuma kula da ita yadda ya kamata.

Hakeem Baba Ahmed ya kara da cewa hakan na da muhimmanci wajen gudanar da shugabanci yadda ya dace.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin da yake jagorantara taro a fadar Aro Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya jaddada cewa ’yan Najeriya ba za su bari gangamin siyasa ya dauke hankalinsu daga neman muhimman abubuwa kamar tsaro da rayuwa cikin mutunci ba.

Baba-Ahmed ya rufe maganarsa da cewa gudanar da sahihin zaɓe a shekarar 2027 zai kawo ƙarshen abin da ya bayyana a matsayin gazawar shugabancin APC.

PRP ta zargi APC ta shirya tuggu

Kun ji cewa jam’iyyar PRP ta zargi wasu mambobin jam’iyya mai mulki da shirin haddasa rikici domin ruguza ƙoƙarin haɗa kan ’yan adawa gabanin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta yi gargaɗi kan ɗaukar wakilan rumfunan zaɓe da sunanta ba tare da izini ba, tana zargin cewa ana iya amfani da kuɗi wajen rinjayar mambobinta

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262