Dan Takarar Majalisa da Jiga Jigan NDC Sun Sauya Sheka zuwa Jam’iyyar APC

Dan Takarar Majalisa da Jiga Jigan NDC Sun Sauya Sheka zuwa Jam’iyyar APC

  • Jam'iyyar NDC a Bayelsa ta rasa wasu manyan jiga-jiganta, ciki har da ɗan takarar majalisar dokoki da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma
  • Felix Wilson ya ce ya fice daga NDC ne bayan an cire sunansa daga matsayin ɗan takara tare da maye gurbinsa da wanda ya kayar
  • Mataimakin gwamnan Bayelsa, Dakta Peter Akpe, ya tarbi masu sauya shekar tare da buƙace su su yi aiki domin haɗin kan APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yenagoa, Bayelsa - Jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a Bayelsa ta rasa wasu daga daga cikin fitattun mambobinta ana shirin zaben 2027.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa yan siyasar sun watsar da jam'iyyar NDC ne bayan sun sanar da sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a ƙarshen mako.

NDC ta rasa jiga-jiganta a Bayelsa
Shugabannin NDC, Peter Obi, Seriake Dickson, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Seriake Henry Dickson.
Source: Twitter

Musabbabin sauya shekar yan NDC a Bayelsa

Kara karanta wannan

2027: Gwamna Fintiri ya mika fom din INEC ga 'yan takarar majalisar Adamawa

Masu sauya shekar sun ce an yaudare su tare da muzanta su a tsohuwar jam'iyyarsu, lamarin da ya sa suka yanke shawarar komawa APC, cewar The Nation.

Felix Wilson, wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na kujerar majalisar dokokin mazabar Sagbama II, ya jagoranci tawagar masu sauya shekar zuwa APC.

Wilson ya ce matsalolin cikin gida sun ƙi samun mafita bayan an cire sunansa daga matsayin ɗan takara tare da maye gurbinsa da Michael Magbisa.

Ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin jam'iyyar ci gaba, yana mai cewa ya koma cikinta tare da dukkan magoya bayansa da suka kasance tare da shi tsawon shekaru.

Wilson ya ce ya yi farin ciki da yadda APC ta karɓe shi da tawagarsa hannu bibbiyu, tare da yin alƙawarin yin aiki domin ci gaban jam'iyyar da nasararta a zaɓe.

APC ta karbi jiga-jigan NDC zuwa cikinta a Bayelsa
Taswirar jihar Bayelsa da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Tsohon mataimakin shugaban NDC ya koma APC

Tsohon mataimakin shugaban NDC na ƙaramar hukumar Ogbia, Saheed Umar, shi ma ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar tare da bayyana goyon bayansa ga APC.

A cewarsa:

"A matsayina na matashi mai kishin ci gaba, na zaɓi na haɗa kai da jam'iyyar da ke mulki tare da shiga ɓangaren masu nasara. Na zo APC ne domin yin hidima."

Kara karanta wannan

An gano yadda aka bindige jigon APC a kofar gidansu bayan sauya jam'iyyar siyasa

Yayin da yake tarbar su, mataimakin gwamnan Bayelsa, Dakta Peter Akpe, ya buƙace su su yi aiki domin haɗin kan jam'iyyar, ci gaban jihar da kuma ƙarfafa gwamnatin Prosperity Administration, cewar Daily Post.

Delta: Hatsaniya a zaben fitar da gwanin NDC

Mun ba ku labarin cewa dan takarar kujerar Majalisar Wakilai a jam’iyyar NDC, Julius Akbovoka, ya bukaci a gudanar da adalci wajen tantance sakamakon zaben fitar da gwani a jihar Delta.

Ya ce har yanzu bai samu sanarwar hukuma daga jam’iyyar kan sakamakon zaben ba, yana zaman jiran halin da ake ciki bayan ya shiga an fafata da shi a neman takara.

Akbovoka ya yi ikirarin cewa shi ne ya samu mafi yawan kuri’u a rumfunan zaben da aka gudanar saboda haka yana dakon a sanar da shi a hukumance halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com