'Yan Bindiga Sun Rutsa 'Yan Islamiya a Jihar Neja An Sace Dalibai ‘Yan Mata
- ‘Yan bindiga sace ɗalibai mata 12 a wata makarantar Islamiyya a kauyen Maikujeri a yanin Raffi da ke jihar Neja
- Ban da ‘yan matan, an yi gaba da ƙanin mai makarantar Madarasatul Nurul Islam kuma an bindige wani mai babur
- A yanzu hare-haren ’yan bindiga sun tilasta wa mutane a ƙananan hukumomi da-dama barin gidajensu a Neja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - An bayar da rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla ɗalibai 12 a wata makaranta a jihar Neja.
An yi awon gaba da yara a Makarantar Islamiyya ta Madarasatul Nurul Islam da ke ƙauyen Maikujeri, a ƙaramar hukumar Rafi.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun dauke 'yan makaranta a Neja
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Asabar, 31 ga watan Oktoba 2026.
Abin ya faru ne lokacin da yaran ke girbin masara a gonar malaminsu da ke wajen garin.
Wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Adamu ya shaida wa jaridar cewa yaran sun riga sun kama hanyar gida aka ritsa su.
A hanyar komawa gida ne ’yan bindigar suka afka musu, suka yin awon gaba da su.
Wani ma babur ya sha harbin 'yan bindiga
An kuma ruwaito cewa wani mai babur mai suna Tasi’u, wanda ya yi ƙoƙarin tserewa ya sha da kyar domin an harbe shi.
A halin yanzu yana karɓar magani a Asibitin Kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
Wata majiya da ke da kusanci da makarantar ta Kur’ani ta shaida wa wakilinmu cewa mutane 13 ne aka sace a ranar.
Ciki har da ɗalibai mata 12 na makarantar da aka ambata da kuma ƙanin mai makarantar, Malam Mainasara.
Yadda aka yi awon gaba da 'yan makarantar
Ya ce shekarun waɗanda aka sace sun kasance tsakanin tara zuwa 14, kuma an dauke su ne da suka tsaya a bakin wata rijiya.
Sun tsaya ne da nufin su sha ruwa kuma su wanke jiki bayan sun gama aiki a gona.
A cewarsa, ɗaliban suna aikin gona tare da malaminsu ne lokacin da malamin ya samu labarin cewa ’yan bindiga na dosowa yankin.
Ya ce nan take malamin ya umarci ɗaliban da su koma gida, shi ma ya kama hanyar tafiya a kan baburinsa, amma ba su tsira ba.
'Yan bindiga sun hana manoma sakat a Neja
Majiyar ta kuma ce an sace wasu mata daga wata gona a yankin da miyagun ‘yan bindiga suka fitina manoma a karkara a halin yanzu.
Manoma sun gagara shiga gonakinsuna domin su yi girbi a ƙauyukan Mariga irinsu Ragada, Maburya, Mazame, Kuimo da Kura.
Haka lamarin yake a wasu karkarar kamar Inana da Idaci da suke cikin ƙaramar hukumar Rijau.
Abin da 'yan sandan jihar Neja suka shaida
Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ’yan sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya yi alƙawarin tantance bayanan kafin ya bada amsa.

Kara karanta wannan
An farmaki ɗan takarar shugaban ƙasa a wurin cin abinci a Najeriya, an garzaya da shi asibiti
Sai dai kakakin ’yan sandan ya bayyana cewa an ceto wasu mutane, amma bai yi magana kan sace ɗaliban wannan makaranta ba.
Ya ce a ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 12:30 na rana, jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun gudanar da samame.
A dalilin haka aka ceto mutane a kusa da Pandogari, ƙaramar hukumar Rafi a jihar ta Neja.
Yanzu ‘yan sandan sun kuɓutar da mutane shida da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a ranar 28 ga Oktoba a kauyen Mahangi.

Source: Getty Images
Ana neman N50m da aka sace malama
Labari ya zo cewa Arewa ta tsakiya, 'yan bindiga sun sace malamar makaranta kuma matar aure, sun nemi fansar Naira miliyan 50.
Amina Hussaini tana koyarwa ne a makarantar Firamare ta LEA a Kuru ta jihar Nasarawa kafin ta fada hannun miyagun 'yan bindiga.
Rahotanni sun ce an yi garkuwa da ita ne a gidanta a lokacin mai gidanta ya tafi aiki a birni.
Asali: Legit.ng

