‘Dan Majalisar Kano Ya Tuno Alherin da Tinubu Ya Yi wa Buhari a Kokarin Tallar APC

‘Dan Majalisar Kano Ya Tuno Alherin da Tinubu Ya Yi wa Buhari a Kokarin Tallar APC

  • Abubakar Kabir Bichi ya ce Muhammadu Buhari ya lashe zaɓen 2015 ne saboda goyon bayan Bola Tinubu
  • Saboda haka ya buƙaci ’yan Arewa su rama wannan alheri ta hanyar zaɓen shugaban Najeriyan a takarar 2027
  • Hon. Bichi ya ce manyan APC a Kano ta Arewa sun sa burin samun ƙuri’u miliyan ɗaya a zaben shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bichi ta Jihar Kano, ya yi kira da su goyi bayan Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Idan ba don goyon bayan Bola Tinubu ba, Abubakar Kabir Bichi, ya ce marigayi Muhammadu Buhari ba zai samu mulkin Najeriya ba.

Bola Tinubu da Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari wajen taro a Paris da Bola Tinubu yana jawabi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A jaridar Daily Trust aka rahoto shi yana bayanin rawar da Bola Tinubu ya taka har APC ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2015.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya sake neman alfarmar yan Najeriya yayin kamfen a Kaduna

Abubakar Bichi ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa bayan ya sha kaye a yunƙurin baya.

A cewarsa, ya kamata ’yan siyasar Arewa su rama wannan goyon baya ta hanyar tattaro ƙuri’u domin sake zaɓen Tinubu a 2027.

Hon. Bichi ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a garin Bichi.

APC tana harin kuri'u miliyan a Arewacin Kano

Bichi ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki a yankin Kano ta Arewa sun ci burin sama wa Tinubu aƙalla ƙuri’u miliyan ɗaya a badi.

‘Dan majalisar tarayyan ya kuma yi watsi da zargin cewa manufofin gwamnatin Tinubu suna yaƙar muradun mutanen Arewacin Najeriya.

Yake cewa amincewa da ayyuka da gine-gine tituna da sauran ayyukan raya ƙasa a Kano na nuna cewa shugaban ƙasar na tare da su.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Bukatar da Shettima ya nema wajen 'yan Arewa kan tazarcen Tinubu

Ya ƙara da cewa wasu daga ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a Kano ba za su yiwu ba tare da goyon bayan gwamnatin tarayya ba.

Murtala Garo ya wakilci Gwamnan Kano a taron

Tribune ta rahoto cewa Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a taron da aka yi.

Murtala Garo ya buƙaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen su yi aiki tuƙuru domin ganin APC ta yi nasara a zaɓen shekara mai zuwa.

Ya kuma gargaɗi ’yan jam’iyyar da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya, su dage da neman goyon bayan jama'a.

Kiran Darekta Janar na yakin zaben APC a Kano

Shi ma Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bukaci masu yaƙin neman zaɓen su ƙara himma wajen wayar da kan matasa da sauran al’umma a Kano.

Tsohon ministan tarayyan shi ne Darakta janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan Kano na APC a 2027.

Darakta janar ya yi kira da babbar murya ga 'yan APC su guje wa tashin hankali a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Shettima ya kama sunan Atiku a taron APC, ya yi masa tonon silili

Buhari da Tinubu
Muhammadu Buhari ranar da aka rantsar da Bola Tinubu a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bincike ya biyo ta kan gwamnatin Muhammadu Buhari

Ana da masaniya rahoto ya gano cewa ofishin raba tallafin kuɗi ya kasa tantance waɗanda suka karɓi N33.75bn a shekarar 2023.

An gano matsaloli wajen tantance yadda aka kashe wasu kuɗin tallafin da aka raba wa talakawa a gwamnatin baya da ta mai-ci a yau.

Yanzu an buƙaci gwamnati ta yi bayani kan makudan kudin da ba a tabbatar da yadda aka kashe su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng