Sabon Littafin Buhari Ya Dauko Labaran Nasarori, Matsaloli da Badakalolin Mulkin shi

Sabon Littafin Buhari Ya Dauko Labaran Nasarori, Matsaloli da Badakalolin Mulkin shi

  • An kaddamar da littafi mai kundin tarihi uku game da Muhammadu Buhari, wanda ya yi nazari kan rayuwarsa, aikin soja da shugabancinsa
  • Littafin mai suna The Making of Muhammadu Buhari: The Authorised Biography ya yi bayani kan nasarorin da gazawar gwamnatinsa a 2015-2023
  • Marubucin littafin, Udo Yakubu, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu da rabi yana bincike domin gabatar da tarihin tsohon shugaban Najeriyan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - An kaddamar da wani sabon littafi tarihi mai kundin uku da ya yi nazari kan rayuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Littafin ya kawo labarin tarihin aikinsa na soja, gwagwarmayarsa a siyasa da kuma nasarori da gazawar gwamnatinsa na tsawon shekaru takwas.

Muhammadu Buhari
Marigayi Muhammadu Buhari da Muhammadou Issoufou a Daura Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Littafin 'The Making of Muhammadu Buhari'

Premium Times ta ce an kaddamar da littafin mai suna The Making of Muhammadu Buhari: The Authorised Biography a birnin Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba gawurtaccen lauya lambar yabo ta 2 a daraja da mutum zai iya samu

Wani masani kuma mai bincike, Udo Yakubu, ya rubuta littafin, yayin da kamfanin May Publishing Ltd ya buga shi shekaru daya da rabi da rasuwar shi.

Littafin ya bi diddigin rayuwar Buhari tun yarintarsa a Daura, jihar Katsina, zuwa lokacin da ya shiga aikin soja har zama shugaban ƙasa a mulkin soja.

Tsohon shugaban Nijar ya yi magana wajen kaddamarwa

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da littafin, tsohon shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou, wanda ya jagoranci taron, ya yabi wannan aiki da aka yi.

Issoufou ya bayyana littafin a matsayin muhimmin gudummawa ga tarihin Najeriya, ya ce zai taimaka wa al'ummomi masu zuwa su fahimci tarihin shi.

Za a fahimci shugabancin Buhari, nasarorinsa da kuma ce-ce-kucen da suka dabaibaye rayuwarsa.

Shugaba Issoufou ya ce marigayi Buhari yana da matsayi na musamman a tarihin Nijar, ya bayyana irin kusancin da ke tsakaninsa da al'ummar ƙasarsa.

Kara karanta wannan

Jonathan ya fito da sabuwar magana kan dalilinsa na mika mulki ga Buhari cikin sauki

Kashim Shettima ya yabi halayen Muhammadu Buhari

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce ainihin abin da ke nuna nagartar shugaba shi ne halayensa da yadda yake gudanar da aikin gwamnati.

Dr. Aliyu Modibbo Umar, mai ba shugaban ƙasa shawara kan ayyuka na musamman a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, ya wakilci Shettima a taron.

Ya ce Buhari ya nuna halayen kirki a rayuwarsa mai sauƙi, ladabtar da kai da kuma kishin hidimar al'umma.

Da yake magana, Shettima ya bayyana marigayi Buhari a matsayin fitaccen mutum a tarihin siyasar Najeriya, wanda ya bambanta da sauran shugabanni.

An dauki lokaci ana kokarin rubuta tarihin Buhari

Marubucin littafin ya ce ya shafe sama da shekaru biyu da rabi yana gudanar da bincike, tattaunawa da mutane, rubutu, gyara da tantance bayanan da ya tattara.

Udo Yakubu ya ce Buhari da kansa ya amince da aikin rubuta tarihin, kuma ya ba shi damar samun bayanai daga mutane, takardu da sauran abubuwan tarihi.

Kara karanta wannan

An sha mamaki da aka gano tsohon shugaba Jonathan yana da mata 2 bayan shekaru

Ya ce littafin ya yi nazari kan sauyin da Buhari ya samu daga jami'in soja har ya zama shugaban ƙasa zuwa ɗan siyasa da ya sha tsayawa takara kafin ya yi nasara.

Yakubu ya ce rasuwar Buhari a 2025 ta kawo ƙarshen damar sake tattaunawa da shi kai tsaye ko neman ƙarin bayani daga gare sa, amma hakan bai tsaida aikin ba.

Littafin ya tabo nasarorin da gwamnatin marigayin ta samu da kuma inda raunin ‘dan adam ya fito.

Udo Yakubu ya ce:

"Akwai sassan da suka nuna nasarori. Akwai kuma waɗanda suka yi nazari kan gazawa.
Wasu za su faranta ran masu kaunarsa, wasu kuma za su sa su ji ba daɗi. Haka abin yake ga masu sukarsa. Wannan shi ne sakamakon ƙoƙarin bayyana rayuwar mutum gaba ɗaya."

Abubuwan da littafin tarihin Buhari ya ƙunsa

An raba littafin zuwa kundin tarihi uku, inda kowannensu ya mayar da hankali kan wani mataki na rayuwar Buhari da aikinsa na gwamnati da yake raye.

Kundin farko ya yi bayani kan asalin iyalinsa, yarintarsa a Daura, karatun aikin soja, rawar da ya taka a yakin basasar Najeriya da mulkin soja da ya yi.

Kara karanta wannan

Dubban mutane sun samu tallafin abinci, babura da injunan niƙa daga Tinubu

An ji manufofin gwamnatinsa da ce-ce-kucen da suka dabaibaye mulkinsa, kifar da gwamnatinsa a 1985 da kuma tsare shi Janar Ibrahim Babangida ya yi.

Kundin ya kuma bayyana yadda ya dawo siyasa, takararsa a zaɓukan 2003, 2007 da 2011, kafa APC da kuma haɗin kan siyasa da ya taimake shi a 2015.

Kundi na biyu ya yi nazari kan gwamnatin farar hula ta Buhari daga shekarar 2015 har zuwa 2023.

Sai kundi na uku ya yi cikakken nazari kan tarihin mulkinsa a fannonin tsaro, tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, da irinsu yaƙi da rashin gaskiya.

An duba harkokin ƙasashen waje, gyaran hukumomi, manufofin jin daɗin al'umma da haɗin kan ƙasa.

Marigayi Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari a Eagle Square ranar da aka rantsar da shi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Surukin Muhammadu Buhari yana takara a Kaduna

A zaben 2027, ana da labari Muhammad Turad Sha’aban zai gwabza da sanata mai-ci da tsohon gwamna a wajen takarar Majalisar dattawa a NDC.

Turad Sha’aban yana takarar kujerar Sanatan Arewacin Kaduna, inda yake fatan doke Sanata mai-ci Khalid Ibrahim Soba da Mukhtar Ramalan Yero.

Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun gana da surukin na marigayi Muhammadu Buhari, aka kaddamar masa da ofishin yakin neman zabe a garin Zariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng