Shettima Ya Kama Sunan Atiku a Taron APC, Ya Yi Masa Tonon Silili

Shettima Ya Kama Sunan Atiku a Taron APC, Ya Yi Masa Tonon Silili

  • Kashim Shettima ya kama sunan Atiku Abubakar a wajen kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar APC a 2027
  • Mataimakin shugaban ƙasar ya tuna yadda Tinubu ya goyi bayan Nuhu Ribadu a 2011 da Muhammadu Buhari a zaɓen 2015 da 2019
  • Shettima ya yi amfani da tarihin haɗin gwiwar Tinubu da ’yan siyasar Arewa wajen ƙarfafa hujjar cewa yankin ya ci gaba da goyon bayan sake zaɓen shugaban ƙasar a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Kashim Shettima ya tuna yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taimaka masa a siyasa tare da ba shi damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2007.

Shettima ya soki Atiku
Atiku Abubakar tare da Kashim Shettima Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Shettima ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 24 ga watan Oktoban 2026 yayin bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Kaduna, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Taron Kaduna ya yi albarka, Uba Sani ya fadi hanyar da za su saka wa Tinubu

Ya ce tarihin goyon bayan da Tinubu ya bai wa fitattun ’yan siyasar Arewa wajen neman shugabancin ƙasar ya nuna irin alaƙar da ke tsakaninsa da yankin, don haka ya kamata Arewa ta ci gaba da mara masa baya a zaɓen 2027.

Shettima ya ce Tinubu ya ba Atiku mafaka a siyasa

Shettima ya tunatar da jama’a cewa Tinubu ya goyi bayan ’yan siyasar Arewa uku a ƙoƙarinsu na neman shugabancin Najeriya.

Ya ambaci Atiku Abubakar a zaɓen 2007, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a yanzu, Nuhu Ribadu, a 2011, da kuma marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2015 da na 2019.

A cewar Shettima, Tinubu ya nuna tsawon shekaru cewa yana da alaƙa ta siyasa da Arewa, saboda goyon bayan da ya bai wa ’yan yankin a lokuta daban-daban, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Da yake magana kan Atiku, Shettima ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nemi taimakon Tinubu bayan rikicinsa da jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Buhari ta wulakanta Tinubu duk da sadaukarwar da ya yi mata

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu mutum ne da ya daɗe yana nuna goyon baya ga Arewa sosai.
“Yana da muhimmanci a tuna cewa lokacin da aka matsa wa tsohon mataimakin shugaban ƙasarmu, Atiku Abubakar, aka kuma kore shi daga PDP, ya garzaya wurin ‘Zakin Bourdillon’, wanda ya ba shi mafaka da goyon bayan siyasa, tare da damar tsayawa takarar shugaban ƙasar nan a 2007,” in ji Shettima.

Ya tuna goyon bayan Tinubu ga Ribadu da Buhari

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tuna yadda Tinubu ya goyi bayan Nuhu Ribadu a ƙoƙarinsa na neman shugabancin Najeriya a 2011.

Shettima ya ce daga baya Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙin neman zaɓen Muhammadu Buhari, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a​ 2015, sannan ya sake samun nasara a zaɓen 2019.

Shettima ya yi wa Atiku shagube
Kashim Shettima tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

APC ta zargi Atiku da karairayi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam’iyyar APC ta zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da yada karairayi game da kamfen dinta a Kaduna.

APC na zargin Atiku Abubakar da shirya amfani da bidiyoyin bogi da takardun ƙarya domin ɓata taron buɗe kamfen shugaban ƙasa a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng