Zaben 2027: Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Sanatan APC, Ta ba Tsohon Gwamna Nasara

Zaben 2027: Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Sanatan APC, Ta ba Tsohon Gwamna Nasara

  • Mai shari’a Inyang Ekwo ya tabbatar da cewa Gabriel Suswam ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar ranar 18 ga Mayun 2026
  • Kotun ta soke sauya sunan Suswam da APC ta yi, inda ta bayyana matakin a matsayin wanda ya saɓa wa dokokin zaɓe da kundin tsarin mulki
  • Ta umarci APC da ta aika sunan Suswam ga INEC a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na APC na kujerar Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas.

Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yanke hukuncin ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026 a shari’ar da aka yi wa alama da lamba FHC/ABJ/CS/1470/2026.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba; kotu ta dauki mataki kan matsalar auren Gwamna Abba

Suswam ya yi nasara a kotu
Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam Hoto: Gabriel Suswam
Source: Twitter

Suswam ne ya shigar da ƙarar a kan APC, Sanata mai ci Emmanuel Udende da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), cewar rahoton jaridar The Punch.

Dalilin da ya sa Suswam ya garzaya kotu

Tsohon gwamnan ya shigar da ƙarar ne domin ƙalubalantar matakin APC na cire sunansa tare da maye gurbinsa da na Udende, duk da cewa shi ne ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

An gudanar da zaɓen ne ranar 18 ga Mayun 2026, inda rahotanni suka nuna cewa Suswam ya samu ƙuri’u 131,083, yayin da Udende ya samu ƙuri’u 1,364 kacal.

A cikin ƙarar, Suswam ya nemi kotu ta soke matakin sauya sunansa, tare da tilasta wa APC da INEC amincewa da shi a matsayin ɗan takarar da jam’iyyar ta tsayar bisa ƙa’ida.

Kotun ta soke sauya sunan Suswam

A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, Mai shari’a Ekwo ya amince da muhimmin ƙorafin Suswam, inda ya tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a ranar 18 ga Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Kotun ta kuma bayyana cewa sauya sunan Suswam da APC ta yi ya saɓa wa doka, musamman tanade-tanaden Dokar Zaɓe da kuma Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.

Mai shari’a Ekwo ya ce Sanata Emmanuel Udende da APC sun kasa gabatar da hujjojin da za su karyata bayanan Suswam da kuma rahoton INEC, wadda ta sanya ido kan zaɓen fidda gwani, jaridar The Sun ta kawo labarin.

Umarnin da kotu ta bai wa APC

Bayan tabbatar da nasarar Suswam, kotun ta umarci APC da ta aika sunansa ga INEC a matsayin halastaccen ɗan takararta na kujerar Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas a zaɓen 2027.

Kafin ta fara sauraron muhimman batutuwan ƙarar, kotun ta kuma yi watsi da ƙorafe-ƙorafen farko da waɗanda ake ƙara suka gabatar domin neman a yi watsi da shari’ar.

Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa waɗannan ƙorafe-ƙorafen ba su da tushe, don haka ba su cancanci a amince da su ba.

Gabriel Suswam ya yi nasara a kotu
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sanata ya gayawa APC gaskiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan APC mai neman komawa majalisar dattawa daga jihar Kano, ya amince cewa wahalar tattalin arziƙin da ta biyo bayan gyare-gyaren Shugaba Bola Tinubu ta fusata masu zaɓe a Arewacin Najeriya.

Sanata Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu kuma ɗan takarar APC a zaɓe mai zuwa, ya yi gargaɗin cewa dole ne jam’iyyar ta sake kusantar talakawa gabanin zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng