Bincike Ya Tono Matsala a N37bn da Aka Ce Gwamnatin Tinubu da Buhari Sun Raba wa Talakawa
- NCTO ya gagara tabbatar da waɗanda suka karɓi N33.75bn da aka raba wa talakawa a shekarar 2023
- An kuma gano wasu biliyoyin Naira da aka biya ba tare da cikakkun takardu da za su iya zama hujja ba
- Babban mai binciken kuɗi a gwamnati ya buƙaci a maido wasu kudin da ake cewa an rabawa talakawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - A shekarar 2023 Ofishin NCTO mai alhakin tura wa talakawa kudi ya yi ikirarin kashe N33bn a gidaje miliyan 3.29 a jihohi 35.
Duk da wadannan makudan kudi da aka kashe, ofishin bai iya bada bayanan talakawan da yake cewa su ne suka amfana da rabon ba.

Source: Getty Images
Premium Times ta ce babu bayanan da za su nuna marasa shi da marasa galihu sun ci moriyar kudin da Gwamnatin tarayya ta raba.
NCTO ya ki ba masu bincike damar samun rahoton bankin da ake bukata domin iya gane kudin da aka batar a wancan lokaci.
UDME ya duba aikin Babban mai binciken kudi na Gwamnatin tarayya, ya sanar da abin da ya gabo a wani rahoto da ya fitar.
Cibiyar ‘yan jarida ta CJID karkashin aikin UDEME ta yi kokarin duba kudin da aka ce an kashe amma aka ki bada hadin-kai.
Binciken yana cikin kokarin da ake yi na gano gaskiyar yadda NCTO ta yi aiki daga 1 ga watan Junairu 2023 zuwa karshen Disamba.
NCTO ya buge da yin inda-inda
NCTO bai iya bada amsar binciken da ake yi masa ba, a inda ya bada amsa kuwa, za ga cewa amsar ba ta wadatar da hukuma ba.
Tsarin rabon kudin ya yi aiki ne lokacin Sadiya Farouk tana ministar yaki da talauci a gwamnatin Muhammadu Buhari a wa’adinsa na biyu.
An cigaba da shirin taimaka wa da tallafi bayan Tinubu ya nada Betta Edu. Amma daga baya dole aka tsige ministar daga kan kujera.
Kwanaki kadan bayan an dakatar da Halima Shehu saboda zargin karkatar da kudi, sai shugaba Tinubu ya tsaida aikin NCTO.
An saba ka'ida wajen tura wa talakawa kudi
Daga cikin ka’idojin da aka taka akwai rashin halatta a tura kudi ga mutum dabam da wanda sunan shi yake cikin takarda.
Ana so takardu su yi cikakken bayanin dalilin aika kudi saboda saukaka bincike idan ta kama.
Takardun banki da suka nuna an kashe sama da N30bn a gidaje miliyan 3.2 ba su dauke da bayanan wadanda suka amfana.
An yi kokarin amfani da REMITA domin samun karin bayani amma jami’an NCTO suka yi ta kawo cikas wajen yin binciken.
Odita-Janar ya ce idan ba a bada dama an yi bincike ba, za a yi zargin cewa an yi amfani da dukiyar jama’a an yaudari mutane.
A na shi shawarar, Odita Janar ya bada shawarar a taso Abdullahi Imam ya yi bayanin inda suka kai kudin kuma a maido su.

Kara karanta wannan
A lokacin da ake rokon talaka ya kara hakuri, an saya wa matasan APC motocin 'N1bn'
Sauran laifuffukan da ake zargin an aikata
Ka’ida ce cewa kafin a ba marasa galihu kudi, dole a bincike su. Ofishin gwamnatin tarayyan bai yi la’akari da hakan ba.
Bayan nan, NCTO ya aika kudi har N4.6bn amma babu takarda. Saboda haka aka bukaci a san yadda za a dawo da biliyoyin.
Akwai N3.09bn da aka tura wa jihohi da sunan za daura wasu talakawa a wannan tsari. Har yau akwai alamar tambaya a nan.
Ofishin na NCTO ya iya kawo hujjar cewa ya raba N2.74bn a jihohi 34, sai dai akwai miliyoyin da ba a san ina suka shiga ba.
Dogon rahoton ya nuna gaba daya akwai ta-cewa a kan yadda aka yi da kudin a gwamnatin baya.

Source: Facebook
Ana binciken wasu jagororin 'yan adawa
Labari ya zo kafin yanzu cewa hukumar CCB tana binciken manyan da ake zargi da ɓoye kadarori da kamfanoninsu a ƙasashen waje.
Lambobin Peter Obi da kuma Bukola Saraki da David Mark da suka taba rike Majalisar Dattawa sun fito a badakalar Panama da Pandora.
Bayan ‘yan adawan da ake bincike, lamarin ya shafi har da wani ‘dan siyasan Najeriya da yanzu yana kabari.
Asali: Legit.ng


