Zaben 2027: Gwamna Ya Gano Gaskiya, Ya Yi Gargadi Mai Zafi ga 'Yan Siyasa
- Gwamna Sheriff Oborevwori ya soki ’yan siyasar da ke kai ’ya’yansu ƙasashen waje domin tsaro, amma suke amfani da yaran wasu wajen rikicin siyasa
- Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin gangamin APC a ƙananan hukumomin Warri South da Uvwie, inda ya gabatar da ɗansa ga mahalarta taron
- Oborevwori ya kuma bayyana ayyukan tituna da gadoji da gwamnatinsa ta gudanar, ciki har da gadar sama ta PTI da DSC da ke Warri-Uvwie
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya gargadi ’yan siyasa kan amfani da ’ya’yan wasu mutane a matsayin ’yan daba, yayin da suke kai nasu ’ya’yan ƙasashen waje domin samun tsaro.
Oborevwori ya yi wannan kira ne a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026 yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyya da mazauna ƙananan hukumomin Warri South da Uvwie na jihar Delta.

Source: Facebook
Gwamnan ya yi amfani da gangamin yaƙin neman zaɓen All Progressives Congress (APC) wajen nuna wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta gudanar tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.
Gargadin da ya yi wa ’yan siyasa
Yayin da yake jaddada aniyarsa ta tabbatar da gudanar da harkokin siyasa cikin lumana a jihar, Oborevwori ya bukaci shugabannin siyasa su kasance masu ɗaukar nauyin ayyukansu.
Ya yi Allah wadai da wasu ’yan siyasa da ke kai ’ya’yansu ƙasashen waje domin kare lafiyarsu, amma suke amfani da yaran wasu mutane wajen aikata rikicin siyasa.
Gwamnan ya bayyana wannan hali a matsayin rashin adalci ga al’umma, inda ya bukaci shugabannin siyasa su kare matasa maimakon jefa su cikin haɗarin da ba dole ba.
A matsayin misali, Oborevwori ya ce nasa ’ya’yan suna nan a Najeriya, kuma suna shiga harkokin siyasa cikin mutunci da sanin ya kamata.
Domin ƙarfafa wannan saƙo, gwamnan ya gabatar da ɗansa, Sheriff Jnr, ga dimbin mutanen da suka halarci gangamin.
Matakin ya zo ne domin nuna cewa ya kamata a gudanar da siyasa cikin mutunci, ɗaukar nauyi da kuma girmama rayuwar bil’adama.
Ya bukaci zaman lafiya da juriya
Oborevwori ya ce bambancin ra'ayin siyasa bai kamata ya zama sanadin barazana ga zaman lafiya da ci gaban jihar ba.
Ya bukaci mazauna jihar su rungumi juriya, tare da bai wa kowa damar amfani da haƙƙinsa na dimokuraɗiyya ba tare da tsoratarwa ko tashin hankali ba.
Ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta gudanar
A yayin taron, gwamnan ya kuma bayyana wasu manyan ayyukan more rayuwa da gwamnatinsa ta gudanar, musamman gadar sama ta PTI da ta DSC.
Ya ce waɗannan ayyuka sun taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa tare da rage lokacin da matafiya ke ɗauka a kan hanyar Warri zuwa Uvwie.
"A yanzu, tafiye-tafiyen da a baya kan ɗauki sa'o'i da dama ga matafiya sun ragu sosai. Wannan sauyi ya nuna amfanin shugabanci mai manufa.” In ji shi.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu
Ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta rayuwar al'ummar jihar ta hanyar gina da gyara tituna, gadoji da kasuwanni, tare da aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa matasa.

Source: Original
Damuwar Jonathan kan zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa mai girma Goodluck Jonathan ya nuna damuwa kan alkiblar da Najeriya ke bi gabanin babban zaɓen 2027.
Goodluck Jonathan ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin haƙurin siyasa, tashin hankali da hamayyar ƙabilanci na iya yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasar.
Asali: Legit.ng

