Kano: Abba Ya Tara Manyan APC da ke Rikici da Juna, Sun Yi Zaman Sulhu

Kano: Abba Ya Tara Manyan APC da ke Rikici da Juna, Sun Yi Zaman Sulhu

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sasanta Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, da Abubakar Kabir Bichi bayan rikicin siyasa tsakaninsu
  • Gwamnan ya bukaci Barau, Bichi da magoya bayansu su ajiye dukkanin korafe-korafensu, su hada kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaben 2027
  • Yusuf ya ce rashin jituwa na daga cikin harkokin siyasa, amma bai kamata a bar ta ta kawo rarrabuwar kai tsakanin ’yan jam’iyya ko ta kawo cikas ga shirye-shiryen zaben 2027 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Abba Kabir Yusuf ya sasanta Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, bayan wani rashin jituwa na siyasa tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Tana sama tana dabo kan shirin kirkirar wasu jihohi, Gwamna ya hango matsala

Ganawar sulhun ta gudana ne a Abuja da sanyin safiyar Laraba, inda ta dauki kusan sa’o’i biyu ana tattauna hanyoyin kawo karshen rashin jituwar da kuma karfafa hadin kai a cikin jam’iyyar APC ta Kano.

Lokacin sasanta 'yan APC a Kano
Abba Kabir Yusuf a tsakiyar Barau Jibrin da Abubakar Bichi. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Matakan da Abba ya dauka

A sakon da Sanusi Bature ya wallafa a Facebook, gwamnan ya bukaci Barau da Bichi da magoya bayansu su ajiye dukkanin korafe-korafe tare da hada kai domin amfanin jam’iyyar.

Punch ta rahoto cewa gwamnan ya ce nasarar APC a dukkan matakai na bukatar hadin kai, fahimtar juna da jajircewar shugabanni da ’yan jam’iyyar.

Abba Kabir Yusuf ya kuma bukaci magoya bayan shugabannin biyu da su guji kalaman batanci, bata suna da duk wani mataki da ka iya kara raba kan ’yan jam’iyyar.

Ya ce:

“Daga yanzu, ba na son wani daga cikin magoya bayanku ya fito yana zagin wani. Dole ne mu dakatar da wannan bata lokaci da ba dole ba.”

Kara karanta wannan

'Illar da rikicin Zamfara zai yi ga Tinubu, Yari, Matawalle da Dauda Lawal'

Kira a hada kai kafin 2027

Gwamnan ya jaddada muhimmancin hada kai domin samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnatin Kano da sauran ’yan takarar APC a babban zaben 2027.

Ya ce sabanin ra’ayi wani bangare ne na harkokin dimokuraɗiyya, amma bai kamata irin wadannan sabanin su kawo cikas ga hadin kan jam’iyya, zaman lafiyarta da ci gabanta ba.

Zaman lafiya ya samu a APC

A jawabansu daban-daban bayan ganawar, Barau Jibrin da Abubakar Bichi sun gargadi magoya bayansu da su guji duk wani abu da zai kara rura rikicin cikin gida a APC.

Sanata Barau Jibrin
Lokacin da Barau Jibrin ya karbi masu sauya sheka. Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Shugabannin biyu sun kuma bayyana ci gaba da goyon bayansu da biyayyarsu ga jam’iyyar, tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan shiga tsakani domin sasanta tsakaninsu.

Sanarwar gwamnatin Kano ta ce sulhun ya samu amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da Gwamna Yusuf ya tabbatar wa shugabannin jam’iyyar cewa APC a Kano a shirye take domin fafutukar samun nasara a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu

Buba ya caccaki APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa jigon jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya zargi APC da amfani da duk wata hanya wajen dakile ayyukan jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027.

Ya bayyana hakan ne a wata hira a ranar Talata, kwanaki 100 kafin zaben 2027, inda ya ce ’yan adawa suna fuskantar cikas yayin da suke shirye-shiryen tunkarar zaben.

Ya yi zargin cewa akwai kokarin raunana ’yan adawa da kuma sanya musu wahala wajen gudanar da yakin neman zabe a fadin kasar, yana mai cewa hakan na sanya cikas a kan hanyar dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng