Sheikh Pakistan Ya Kare Ayyukan Tinubu a Kano, Ya Yi Kuskuren Bayanai kan N9trn
- Tsohon shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da ayyukan naira tiriliyan tara a Kano
- Sai dai bincike bai gano hujjojin da ke tabbatar da wannan ikirari ba, ciki har da kuɗin ayyukan hasken rana da aka ambata
- Binciken ya gano cewa gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 70 domin samar da hasken rana a manyan makarantu 12
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon shugaban hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya fadi kokarin da Bola Tinubu ya yi a Kano.
Pakistan ya ce Tinubu ya cancanci a sake zaɓensa saboda ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar da kuma abin da ya kira inganta tsaro.

Source: Facebook
Abin da Sheikh Pakistan ya ce
Pakistan ya bayyana hakan ne a wata hira da DCL Hausa inda ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta aiwatar da ayyukan da kuɗinsu ya haura naira tiriliyan tara a Jihar Kano.
Ya ambaci samar da na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana ga Jami’ar Northwest da ke Kano, wanda ya ce ya ci Naira biliyan shida, da kuma wani tsarin hasken rana na gidan rediyon Radio Kano, wanda ya ce ya ci Naira biliyan biyu.
Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta samar da waɗannan na’urori duk da cewa Jami’ar Northwest mallakar gwamnatin Jihar Kano ce.
Pakistan ya ce zai ci gaba da goyon bayan gwamnatin Tinubu saboda ya yi imanin cewa shugaban ya nuna ƙwarewar jagoranci kuma ya cancanci wani wa’adi domin kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara.
Pakistan ya kuma ambaci hanyar Kaduna zuwa Abuja, yana mai cewa matafiya sun fuskanci matsalolin tsaro sosai a kan hanyar a baya, amma yanayin ya inganta a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Source: Facebook
Gaskiyar lamari kan ayyukan Tinubu a Kano
Sai dai wani bincike da Daily Trust ta gudanar kan bayanan da jama’a za su iya samu, ciki har da dandalin GovSpend, bai gano wata hujja da za ta tabbatar da ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da ayyukan da suka kai naira tiriliyan tara a Jihar Kano ba.
Binciken ya kuma gano cewa babu rahotannin da jama’a za su iya samu da suka tabbatar da ƙaddamar da ayyukan samar da wutar lantarki ta hasken rana da Pakistan ya ambata, ko kuma kuɗin da ya ce an kashe a kansu.
Abin da binciken ya gano
Gwamnatin tarayya, ta hannun Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund), ta ware naira biliyan 70 domin aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana ta hanyar ƙananan cibiyoyin rarraba wuta a wasu manyan makarantu a faɗin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya amince da aikin a ƙarƙashin shirin tallafin TETFund na shekarar 2025.
Da yake jawabi a taron farko na TETFund da masu ruwa da tsaki, shugaban kwamitin amintattu na asusun, Aminu Bello Masari, ya ce shirin zai samar da makamashi mai ɗorewa ga manyan makarantu 12 da aka zaɓa.
Makarantun sun haɗa da Jami’ar Northwest da ke Kano, Jami’ar Sojojin Najeriya da ke Biu a Jihar Borno, Jami’ar Ambrose Alli da ke Jihar Edo, Jami’ar Ilimi ta Alvan Ikoku da ke Owerri a Jihar Imo, da Jami’ar Jihar Legas.
Hukunci: Ba a tabbatar da ikirarin ba
Binciken ya gano cewa babu hujjar da za a iya tantancewa da za ta tabbatar da ikirarin cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar da ayyukan naira tiriliyan tara a Jihar Kano.

Kara karanta wannan
Taohon shugaban APC na Kano ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga wurin kamfen Tinubu
Duk da cewa an sanar da shirin samar da hasken rana da gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyi a Jami’ar Northwest, bayanan da ake da su ba su tabbatar da kuɗin ayyukan da Pakistan ya ambata ko ikirarin naira tiriliyan tara ba.
SERAP ta maka Tinubu a kotu
Mun ba ku labarin cewa SERAP ta shigar da ƙara kan gwamnatin tarayya bisa zargin rashin bin ƙa’ida wajen rabon kudaden tallafi.
Rahoton babban mai binciken kuɗi na tarayya ya nuna akwai kuɗaɗen da ba a samu isassun takardun tabbatar da biyan su ba.
Ƙungiyar ta nemi kotun ta umarci gwamnati ta bayyana yadda aka kashe kuɗin, ta gudanar da bincike tare da dawo da duk kuɗin da aka karkatar ba bisa ƙa’ida ba.
Asali: Legit.ng

