Duk da Arangama a Kamfen Uba Sani, Gwamna Ya Ɗauka wa Tinubu Alƙawari

Duk da Arangama a Kamfen Uba Sani, Gwamna Ya Ɗauka wa Tinubu Alƙawari

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce APC za ta tattara ƙuri’u domin bai wa Shugaba Bola Tinubu kashi 70 cikin 100 a zaɓen 2027
  • Ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC ranar Alhamis
  • Gwamnan ya ce gwamnatin Tinubu ta amince da manyan ayyukan raya ƙasa, ciki har da jami’o’i huɗu da tallafin N20bn ga Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana shirin APC a jihar domin nasarar Bola Ahmed Tinubu.

Uba Sani ya ce APC a jihar za ta yi ƙoƙarin tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu kashi 70 cikin 100 na ƙuri’un da za a kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a jihar Kano ya yi ƙamari, an aika saƙon gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari

Gwamna Uba Sani ya dauka wa Tinubu alkawari
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da Bola Tinubu. Hoto: Uba Sani, Dada Olusegun.
Source: Twitter

Kwarin guiwar da Uba Sani ya nuna

Uba Sani ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC, cewar TheCable.

Gwamnan ya nuna kwarin gwiwarsa kan damar da jam’iyyar ke da ita a zaɓukan da ke tafe, inda ya ce taron jama’a da suka halarta ya nuna irin goyon bayan da APC ke da shi a jihar.

Ya ce:

“Yawan jama’ar da suka fito a yau ya nuna irin goyon bayan da al’ummarmu ke da shi ga jam’iyyarmu da kuma amincewarsu da shugabancinmu.”

Uba Sani ya yaba wa gwamnatin Tinubu

Gwamnan ya ce al’ummar Kaduna za su rama goyon bayan da gwamnatin Tinubu ta ba jihar ta hanyar ayyukan more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi da tsaro.

Ya bayyana cewa irin tallafin da jihar ta samu daga gwamnatin Tinubu ba a taɓa samun irinsa ba a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shinkafa da wake: An kafa kwamitin kamfen Tinubu da APC cike da yan adawa

Uba Sani ya ce gwamnatin tarayya ta amince da kafa jami’o’i huɗu a Kaduna, duk da cewa jihar ta nemi guda biyu ne kawai.

Jami’o’in sun haɗa da:

* Jami’ar Ilimi ta Tarayya.

* Jami’ar Kimiyyar Aiwatarwa ta Tarayya da ke Kachia.

* Jami’ar Kimiyyar Shuke-shuke ta Tarayya.

* Jami’ar Fasaha ta Tarayya.

Uba Sani ya yi wa Tinubu alkawari a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna da APC ke mulki a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

An amince da N20bn ga Kaduna

Haka kuma, gwamnan ya ce jihar ta nemi gwamnatin tarayya ta gudanar da wasu ayyukan tituna, ciki har da hanyar Manchok zuwa Bakin Bayi, Zariya zuwa Soba zuwa Pantsega da Jema’a zuwa Gwantu.

Ya kuma bayyana cewa jihar ta nemi a gina layin dogo na cikin gari domin inganta sufuri da haɗin kai tsakanin al’ummomi.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta amince da bayar da tallafin Naira biliyan 20 domin ayyukan ci gaban jihar, cewar Punch.

Ya ƙara da cewa ɗaliban jihar sun amfana da sama da Naira biliyan shida ta hanyar tallafin karatu da sauran shirye-shiryen taimakon ilimi.

Gwamnatin Kaduna ta musanta zargin ADC

An ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta yi magana kan sahihancin wata wasika wacce ta nuna cewa ta hana ADC amfani da filin wasa na Ranchers Bees.

Kara karanta wannan

2027: Arewa ta zama kan gaba da Tinubu ya kara jihohin da zai je kamfen

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Sadiq Mamman Lagos, ya ce wasikar karya ce kuma ba ta fito daga su ba.

Gwamnatin ta bukaci jama’a da su yi watsi da takardar tare da guje wa yada labaran karya da ka iya haifar da rudani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.