Mahara Dauke da Makamai Sun Kutsa Gidan Tsohon Kyaftin Din 'Yan Wasan Najeriya

Mahara Dauke da Makamai Sun Kutsa Gidan Tsohon Kyaftin Din 'Yan Wasan Najeriya

  • An kai wa tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Segun Odegbami, hari tare da sararsa da adduna a gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun
  • Rahotanni sun ce wasu mutane uku ɗauke da makamai ne suka kutsa gidansa da ke Ibara GRA da sanyin safiyar Juma’a
  • ’Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa an sallami Odegbami daga asibiti bayan ya samu kulawar likitoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun, Nigeria - An ruwaito cewa wasu mahara sun kai wa tsohon kyaftin ɗin Super Eagles kuma fitaccen mai gudanar da harkokin wasanni, Segun Odegbami, hari tare da sararsa da adduna a Abeokuta, Jihar Ogun.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, lokacin da wasu mutane uku ɗauke da makamai suka kutsa gidansa da ke yankin Ibara GRA a Abeokuta.

Kara karanta wannan

2027: Magoya bayan APC sun yi takansu da rigima ta ɓarke a wurin yakin neman zaben gwamna

Segun Odegbami
Tsohon Kyaftin ɗin Super Eagles ta Najeriya, Segun Odegbami Hoto: Super Eagles
Source: Getty Images

Daily Trust ta ruwaito cewa Odegbami, wanda aka fi sani da Mathematical, kuma mamallakin gidan rediyon wasanni na Eagles 7 Sports Radio 103.7 FM, ya samu raunuka a yayin harin.

Majiyoyi sun ce maharan sun fara kai wa ma’aikatan gidansa da direbansa hari kafin daga bisani suka nufi ɗakin kwanan shi.

Yadda aka farmaki Segun Odegbami

An ce Odegbami, mai shekaru 74, ya yi ƙoƙarin kare kansa lokacin da maharan suka shiga ɗakinsa, lamarin da ya jawo gumurzu mai zafi tsakaninsu.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Lamarin abin takaici ne, mun ji cewa mutanen ɗauke da makamai sun kai farmaki da sanyin safiyar yau (Juma’a), inda suka fara galaba a kan ma’aikatan gidan. Sun tambayi inda Cif Segun Odegbami yake, amma ma’aikatan suka ki fada masu yana gida.
“Amma janareta yana aiki a lokacin. Saboda haka, maharan sun yi zaton dole yana gida, suka yi wa ma’aikatan dukan tsiya, suka samu hanyar shiga ɗakin kwanan Odegbami suka kai masa hari.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya fara garkuwa da mutane a Amurka, 'yan sanda na neman shi

“Da yake bai yarda ya miƙa wuya cikin sauƙi ba, Odegbami ya tare su, lamarin da ya sa maharan suka yi gaggawar tserewa daga wurin, suka bar shi yana zubar da jini sosai.

A cewar mazaunin yankin, an garzaya da shi zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba, inda ya samu kulawar likitoci.

Yan sanda sun tabbatar da harin

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Oluseyi Babaseyi, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Ya ce:

“Nan take ’yan sanda suka bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan yanayin da lamarin ya faru, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata laifin tare da kama su.”

Babaseyi ya kuma tabbatar da cewa an sallami Odegbami daga asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262