Zaben 2027: Bukatar da Shettima Ya Nema Wajen 'Yan Arewa kan Tazarcen Tinubu
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci masu zaɓe a Arewa su haɗa kai domin ganin Bola Tinubu ya sake lashe zaɓe
- Shettima ya tuna yadda Tinubu ya goyi bayan Atiku Abubakar a 2007 da marigayi Muhammadu Buhari a zaɓen 2015 da 2019
- Ya bayyana jami’o’i, ayyukan tituna da hanyoyin jirgin ƙasa da bututun iskar gas a matsayin wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya mika bukatarsa ga masu zabe a yankin Arewacin Najeriya.
Shettima ya buƙaci masu zaɓe a yankin Arewa su haɗa kai wajen mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Source: Facebook
Shettima ya yi wannan kira ne ranar Asabar, 24 ga watan Oktoban 2026 yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Kaduna, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Meyasa Shettima yake so Arewa ta zabi Tinubu?
Mataimakin shugaban kasar ya ce Tinubu ya daɗe yana taimaka wa ’yan siyasar Arewa, ciki har da marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa ya kamata yankin Arewa ya rama goyon bayan da Tinubu ya bai wa ’yan siyasar yankin ta hanyar sake zaɓensa da sauran ’yan takarar APC da ke neman muƙamai daban-daban.
“Mun zo ne domin neman ku sake zaɓar APC a karo na biyu, daga sama har ƙasa,” in ji Shettima.
Shettima ya kare ayyukan gwamnatin Tinubu
A yayin jawabin, Shettima ya kuma kare gwamnatin Tinubu, yana mai cewa ta cimma wasu daga cikin alkawuran da ta ɗauka a muhimman fannoni.
Ya ce ɗaya daga cikin alkawuran da gwamnatin ta ɗauka shi ne dawo da martabar jihar Kaduna a matsayin cibiyar ilimi a Najeriya.
A matsayin misalan ayyukan da ya ce an gudanar a jihar, Shettima ya ambaci kafa Jami’ar Kimiyya ta Tarayya da ke Kachia, mayar da cibiyar ilimi da ke Zaria zuwa Jami’ar Ilimi ta Tarayya, da kuma kafa cibiyar koyon sana’o’i ta jihar a Rigachikun.
A cewarsa, waɗannan matakai na daga cikin ƙoƙarin ƙara inganta ilimi da koyar da sana’o’i a Kaduna.
Ya lissafa manyan ayyuka
Shettima ya kuma ambaci wasu manyan ayyukan more rayuwa da yake cewa gwamnatin Tinubu na ci gaba da aiwatarwa, jaridar TheCable ta kawo labarin.
Daga cikin ayyukan da ya lissafa akwai bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano, layin dogo na Kano–Maradun, hanyar jirgin ƙasa ta Legas–Kano, da kuma babbar hanyar Abuja–Kaduna–Kano.
Ya kuma ce ana ci gaba da aikin babbar hanyar Sokoto–Badagry, wadda a cewarsa za ta buɗe sabbin damar bunƙasa noma da sauran harkokin tattalin arziki a ƙasar.
Shettima ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da damarmaki ga jama’a, musamman a fannin noma da sufuri.

Source: Facebook
Shettima ya yi wa Atiku shagube
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Kashim Shettima ya tuna yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taimaka masa a siyasa tare da ba shi damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2007.
Asali: Legit.ng

