Maganar Zargin Dickson Yana Shirya wa Obi da Kwankwaso Makarkashiya Ta Yi Nisa a NDC
- NDC ta karyata zargin cewa Seriake Dickson na shirin yi wa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso zagon kasa
- Jam’iyyar hamayyar ta ce babu wata yarjejeniya tsakanin tsohon gwamnan Bayelsa da APC kan zaben 2027
- Kakakin NDC ya bayyana zargin da ake yi wa Dickson a matsayin karya marar tushe da abokan adawa suke yadawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jam’iyyar NDC ta musanta zargin cewa jagoranta na kasa, Seriake Dickson, na shirin yi wa yan takararta zagon kasa.
NDC ta ce babu kullaliya tsakanin Sanata Seriake Dickson da Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso a zaben 2027.

Source: Getty Images
Babu zancen cin amanar Peter Obi/Rabiu Kwankwaso
Mai magana da yawun NDC na kasa, Osa Director, ya bayyana zargin a wata sanarwa ranar Litinin a cewar jaridar Premium Times.
Mista Director ya ce, akasin zargin da ake yi Sanata Dickson ba shi da wani shiri na yi wa jam’iyyar APC aiki a zabe mai zuwa.
“Jagoranmu na Kasa, Sanata Seriake Dickson, ba aiki yake yi wa APC a boye ba, kuma ba wakilin wani bangare ba ne.
“Ba shi da wata yarjejeniya ta boye ko a fili da gwamnatin APC mai cike da barna da mugunta,”
- in ji shi.
Ya ce jam’iyyar za ta iya biris da abin da ya kira maganganun banza na teburin mai shayi da suke yawo a kafafen sada zumunta.
Sanarwar ta ce amma NDC ta yanke shawarar karyata zancen domin hana mutane gaskata karya.
“Duk wanda ya san tarihin Sanata Dickson a aikin gwamnati, kuma yana cikin hayyacinsa, ba zai danganta shi da wata yarjejeniyaa boye ta yi wa jam’iyyarsa da dan takararta na shugaban kasa da abokin takararsa, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, zagon kasa ba,”
Mai magana da yawun NDC ya ce Mista Dickson, wanda ke kan kujerar Sanata, zai iya zabar hanya mafi sauƙi ta komawa APC salin-alin.
Seriake Dickson ya zabi ya kafa NDC
Punch ta rahoto shi ya ce Dickson ya zabi hanya mai wahala kuma mai daraja ta gina jam’iyya tare da masu irin ra’ayinsa.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu
Ya ce NDC ce jam’iyyar da za ta ‘yantar da Najeriya daga matsananciyar rikon da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki suke yi.
Mista Director ya yi bayanin yadda Dickson ya shafe shekaru bakwai a Majalisar Dattawa yana yaki da jam’iyya mai-ci.
Director ya kare da cewa:
“Saboda haka, mugunta ce, cin zarafi ne kuma karya ce a danganta sunansa da wata yarjejeniya da APC mai mulki da manyan masu tafiyar da ita.
“Muna sane da cewa waɗannan zarge-zargen marasa tushe sun samo asali ne daga cikin ‘yan adawar siyasa, waɗanda ke kishin yadda farin jinin NDC, karɓuwarta da kuma yaɗuwarta ke ƙaruwa a faɗin Najeriya”

Source: Getty Images
Rabuwa da Kwankwaso za ta taba Abba
A wani labari da mu ka kawo, an ji cewa Adnan Mukhtar Tudun Wada ya ce Gwamnan Kano na fuskantar barazanar shan kaye a 2027.
Matashin ‘dan siyasar ya ce yawo da hular Omo logo kullum-yaumin ba zai ceci Abba Kabir Yusuf ba idan aka shiga filin zabe a shekarar badi.
Malam Adnan ya yi hasashen cewa rabuwar Abba da Rabiu Kwankwaso na iya jefa shi cikin matsala saboda Kanawa ba su son butulci.
Asali: Legit.ng
