Manyan Abubuwa 5 da za Su Faru a 2027 Su Dauki Hankalin Duniya
Bayan zaben Najeriya da ake shirin a shekara mai zuwa, mun hada maku rahoto na musamman a kan abubuwan da ake sa ran za su faru a 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ana sa ran shekarar 2027 za ta zo da manyan al’amura a duniya, ciki har da ƙarin zafin yanayi, sauyin iko a Majalisar Dokokin Amurka da zaɓen shugaban ƙasar Faransa
Haka kuma, za a samu kusufin rana na gaba ɗaya a watan Agusta, yayin da Brazil za ta karɓi bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata.

Source: Getty Images
An wannan labarin, mun hada muku rahoto na musamman kan manyan abubuwa biyar da ake sa ran za su ja hankalin duniya a shekarar 2027.
1. Ƙarin zafin duniya sakamakon El Niño
Ana sa ran shekarar 2027 za ta iya kafa sabon tarihin zafin duniya, sakamakon wani zagayen yanayin El Niño da ake hasashen zai kasance cikin mafi ƙarfi da aka taɓa gani.
El Niño wani yanayi ne da ke faruwa a tekun Pacific kusan duk bayan shekaru biyu zuwa bakwai, wanda ke sauya tsarin ruwan sama a sassan duniya tare da ƙara zafin yanayi.
Wannan yanayi na ƙara tsananta zafin da sauyin yanayi ke haifarwa, lamarin da ke iya jawo matsaloli ga noma da samar da abinci.
Tuni El Niño na wannan shekarar ya fara shafar noman masara a Amurka ta Tsakiya, kamun kifi a Peru, da kuma samar da sukari da shinkafa a yankin Kudu maso Gabashin Asiya.
Kaveh Zahedi na Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa mafi munin tasirin da wannan yanayi zai haifar wa wasu yankuna da farashin abinci na iya kasancewa a gaba.
Hakan na zuwa ne a lokacin da manoma ke fuskantar tsadar kayayyaki sakamakon yaƙin Iran, tare da raguwar tallafin agaji daga ƙasashen duniya.
2. Democrat za ta karɓi ikon a Amurka

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An kai wa fitacciyar 'yar TikTok kuma 'yar Kwankwasiyya hari a Kano
Ana sa ran jam'iyyar Democrat za ta karɓi rinjayen kujeru a majalisun dokokin Amurka biyu a watan Janairun 2027, bayan nasarar da ta samu a zaɓen tsakiyar wa’adin mulki na watan Nuwamba.
Wannan sauyin iko zai iya sauya yadda shugaban ƙasar, Donald Trump, zai gudanar da ragowar shekaru biyu na wa’adinsa, domin 'yan Democrat za su samu damar ƙalubalantar manufofinsa.
Jam'iyyar ta bayyana cewa tana son rage tsadar rayuwa ta hanyar dawo da tallafin inshorar lafiya, soke wasu rage kuɗin kula da lafiya da kuma janye harajin kwastam da Trump ya kakaba.
Haka kuma, tana son kawo ƙarshen yaƙin Iran wanda ya taimaka wajen ƙara farashin man fetur a fadin duniya.
Ana sa ran Hakeem Jeffries zai zama Ba’amurke na farko ɗan Afirka da zai jagoranci Majalisar Wakilai, inda zai samu damar tsara yadda za a tattauna kudurorin jam'iyyar da kuma kula da kasafin kuɗin tarayya.

Source: Getty Images
'Yan Democrat za su kuma iya gudanar da bincike kan zargin cin hanci da rashawa, harkokin kasuwancin iyalan Trump, dokokin shige da fice da yadda aka tafiyar da yaƙin Iran.
3. Zaɓen shugaban ƙasar Faransa
BBC ta wallafa cewa Faransa za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranakun 18 ga Afrilu da 2 ga Mayun 2027, wanda zai kawo ƙarshen wa’adin Emmanuel Macron bayan shafe shekaru 10 yana mulki.
Ana hasashen zaɓen zai kasance mai zafi sakamakon rikicin siyasa, rabuwar kai a tsakanin al'umma da kuma tashin hankalin da ake samu a wasu sassan ƙasar.
Manyan batutuwan da ake sa ran za su mamaye yaƙin neman zaɓen sun haɗa da fansho, shige da fice, tsaro da kuma halin da ake ciki a yaƙin Ukraine.
Haka kuma, zanga-zangar ɗaliban makarantun sakandare na iya tilasta wa 'yan takara bayyana matsayarsu kan matsalolin tsarin ilimi da ayyukan gwamnati.
4. Za a sake samun kusufin rana
A ranar 2 ga Agustan 2027, ana sa ran za a samu kusufin rana na gaba ɗaya, inda wata zai rufe hasken rana na ɗan lokaci, har wasu wurare su yi duhu kamar dare.
Za a iya ganin wannan lamari daga kudancin Spain, amma zai fi bayyana a wasu sassan Arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya.
A tsakiyar hanyar da kusufin zai bi, ana sa ran duhun zai ɗauki sama da mintuna shida, lamarin da zai ba masu sha'awar kallon sararin samaniya damar ganin wani abin al'ajabi.
Kusufin rana na gaba ɗaya yana faruwa ne lokacin da wata ya shiga tsakanin duniya da rana, ya toshe hasken rana tare da jefa inuwarsa a wani ɗan ƙaramin yanki na doron ƙasa.
5. Gasar cin kofin duniya ta mata
Bayan kammala gasar cin kofin duniya ta maza ta 2026, hankalin masoyan ƙwallon ƙafa zai karkata zuwa Brazil, wadda za ta karɓi bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata ta 2027.
Ana sa ran Spain, wadda ta lashe gasar da ta gabata, za ta kasance cikin ƙasashen da ake ganin za su iya lashe kofin.
Taurarin ƙungiyar, Alexia Putellas da Aitana Bonmati, za su kasance cikin manyan 'yan wasan da za a sa ido a kansu.
Sai dai Ingila, wadda ta doke Spain ta lashe gasar zakarun Turai ta mata a bara, da kuma Amurka mai kofuna huɗu, na cikin ƙasashen da za su yi ƙoƙarin kaiwa wasan ƙarshe.
Ana sa ran za a gudanar da wasan ƙarshe a shahararren filin wasa na Maracana da ke Brazil a ranar 25 ga Yulin 2027.
Za a yi zaben Najeriya a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ta cire bayanan masu rijistar zaɓe sama da miliyan 1.6 da ba su inganta ba daga kundin masu zaɓe.

Kara karanta wannan
Amurka ta kara sunayen 'yan Najeriya 24 cikin wasu 157 da za a fatattako daga kasar
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa wannan mataki ya rage adadin masu rijistar zaɓe daga miliyan 103 zuwa sama da miliyan 100.
Ya kuma ce sama da mutane miliyan 10.77 da suka yi sabon rijista sun samu nasarar shiga sahihin kundin masu zaɓe yayin da ake shirin kada kuri'a a 2027.
Asali: Legit.ng


