Makinde Ya Shirya Marawa Atiku Baya a Zaɓen 2027? An Samu Bayanai

Makinde Ya Shirya Marawa Atiku Baya a Zaɓen 2027? An Samu Bayanai

  • Gwamna Seyi Makinde ya yi magana kan rade-radin cewa zai janye takararsa ta shugaban kasa domin marawa Aiku Abubakar baya
  • Kungiyar yakin neman zaben Makinde ta bayyana rahoton a matsayin labaran karya, inda ta zargi APC da yada bayanan da ba su da tushe kan 'yan adawa
  • Rahoton da aka karyata ya yi ikirarin cewa Makinde zai janye takararsa ranar 30 ga Nuwamba, 2026, tare da hada kai da Atiku karkashin ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo – Kwamitin yakin neman zaben Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi martani ta kan rahoton da ke ikirarin cewa gwamnan na shirin janye takararsa ga Atiku Abubakar.

Makinde ya musanta marawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar baya a zaben shugaban kasa a 2027 da ake tunkara a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta ɗauki mataki kan Sarkin Daura bayan ɓullar bidiyonsa da baturiya

Makinde ya karyata shirin marawa Atiku baya
Gwamna Seyi Makinde da Atiku Abubakar. Hoto: Seyi Makinde, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Sanarwar karyata rahoton ta fito ne a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamban 2026, ta shafin X mai alaka da kungiyar yakin neman zaben gwamnan, mai suna @makindedaura, karkashin taken #MakindeDaura2027.

An ƙaryata shirin janye wa Atiku

Kwamitin ya bayyana rahoton a matsayin labaran karya, tana mai cewa babu gaskiya a cikin ikirarin cewa Seyi Makinde zai hakura da takararsa domin Atiku.

Hakan ya biyo bayan wani ikirari da mai sharhi kan siyasa, Lere Olayinka, ya wallafa cewa Makinde, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM zai janye takararsa ranar 30 ga Nuwamba, 2026 da muke ciki.

Olayinka ya kuma yi ikirarin cewa Makinde na tattaunawa kan yadda kungiyar Social Contract Front (SCF) za ta hade da APM domin marawa Atiku baya a karkashin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), a matsayin dan takarar hadin gwiwa.

Makinde ya musanta janye wa Atiku takara
Dan takarar shugaban kasa a APM, Seyi Makinde. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Makinde ya zargi APC da yada labaran karya

Kara karanta wannan

Abin da Nafiu Bala ya fada wa ƴan 'takarar' ADC bayan tara su a Kaduna

A martanin da ta wallafa, kungiyar yakin neman zaben Makinde ta sanya alamar "FAKE NEWS" a kan sakon Olayinka, kafin ta zargi jam'iyyar APC mai mulki da kirkirar labaran karya kan 'yan adawa.

Sanarwar ta ce:

"APC na kara nuna matsananciyar damuwa har ta kai ga yada karya kan 'yan adawa. Seyi Makinde barazana ne da APC ba ta yi tsammanin zai kasance ba.
"Zabe mai zuwa tsakanin 'yan Najeriya ne da APC, kuma 'yan Najeriya za su yi nasara da yardar Ubangiji."

Sai dai kwamitin ba ta yi karin bayani kan batun tattaunawar hadakar siyasa da ake zargin ana yi ba, face karyata rahoton baki daya.

Makinde ya magantu kan shirin yan adawa

A wani rahoto makamancin wannan, mun ruwaito cewa Gwamna Seyi Makinde ya bayyana yiwuwar samar da wata hadakar siyasa tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi gabanin zaben 2027.

Makinde, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da dan jarida Chude Jideonwo wanda aka yada a kafafen sadarwa.

Gwamnan ya bayyana cewa tsarin hadakar da ake tattaunawa a kai ba zai kasance irin tsarin hadakar jam'iyyun adawa ta shekarar 2015 da ta kai ga kafa gwamnatin APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.