Kano: NDC Ta Yi Mamakin Cire Sunan Gwarzo, Ta Faɗi Tabbacin da INEC Ta ba Ta

Kano: NDC Ta Yi Mamakin Cire Sunan Gwarzo, Ta Faɗi Tabbacin da INEC Ta ba Ta

  • Jam’iyyar NDC a Kano ta bukaci mambobinta su kwantar da hankalinsu bayan INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamna
  • Kakakin jam’iyyar, Yusif Fasaha, ya ce INEC ta bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga kwamfuta, kuma za a gyara kuskuren nan ba da jimawa ba
  • Fasaha ya tabbatar da cewa Abdussalam-Gwarzo ya cika dukkan sharuddan takara, yana mai cewa ana sa ran fitar da sabon jerin sunayen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta reshen jihar Kano ta yi martani bayan hukumar IINEC ta fitar da sunayen ƴan takarar gwamna.

NDC ta bukaci mambobinta su kwantar da hankalinsu yayin da ake ce-ce-ku-ce kan rashin sunan ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam-Gwarzo, a jerin sunayen da INEC ta fitar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'Ba a cire sunan Pantami a takara ba': PDP ta kwantar wa masoyanta hankali

An rasa sunan Gwarzo cikin jerin yan takara
Dan takarar gwamnan Kano a NDC, Aminu Abdulsalam Gwarzo. Hoto: Kwankwasiyya Movement.
Source: Twitter

Jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar, Yusif Fasaha, ne ya yi wannan kira cikin wata sanarwa da ya bai wa Punch.

Martanin NDC kan cire sunan Gwarzo a Kano

Fasaha ya ba mambobin jam'iyyar tabbacin cewa matsala aka samu daga hukumar INEC kuma za a gyara komai a kankanin lokaci.

Ya bayyana cewa sun tuntubi hukumar INEC kuma ta fada masu abin da ya jawo aka cire sunan Gwarzo daga jerin yan takarar.

Fasaha ya ce:

“Ina tabbatar muku cewa matsalar ba daga gare mu take ba, ni a matsayina na jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar.”
“Mun tuntubi INEC, kuma sun gaya mana cewa matsalar ta samo asali ne daga kwamfuta, kuma za su gyara ta.
“Saboda haka, kowa ya kwantar da hankalinsa. Daga yanzu zuwa ranar Litinin, za a fitar da wani sabon jerin sunayen da zai ƙunshi sunansa.”

NDC ta ce ɗan takararta ya cika sharuddan INEC

Kara karanta wannan

INEC ta cire sunan Aminu Gwarzo daga jerin 'yan takarar gwamnan jihar Kano a 2027

Fasaha ya bayyana cewa Abdussalam-Gwarzo ya cika dukkan sharuddan da ake buƙata domin tsayawa takarar zaɓen, yana mai jaddada cewa an kammala komai a kan lokaci.

Ya ce:

“Mun ga jerin sunayen, kuma za mu ci gaba da tattaunawa kan wannan batu.”

INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar gwamna 17 a Kano

Majiyoyi daga Premium Times ta lura cewa jerin sunayen ya ƙunshi ‘yan takarar gwamna 17 da mataimakansu daga jam’iyyun siyasa daban-daban.

Sunan Gwamna Abba Yusuf ya bayyana a jerin a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC, tare da mataimakinsa, Murtala Sule-Garo.

Sauran jam’iyyun da aka tantance sun haɗa da ADC, PDP, APGA, BP, AA, AAC, LP, ZLP, SDP, APM, NDP, PRP, APP, DLA da ADP.

INEC ta cire sunan Pantami cikin yan takara

A wani labarin makamancin wannan, INEC ta cire sunayen Farfesa Isa Ali Pantami daga cikin jerin wadanda za su yi takara a zaɓen shekarar 2027.

Daga cikin wadanda aka cire akwai Buruji Kashamu Adebutu daga jerin sunayen ‘yan takarar gwamna na 2027, yayin da ta amince da Kingsley Chinda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.