Ministan Buhari Ya Tube Babbar Riga Ya Tafi Kotu Kare El Rufa'i

Ministan Buhari Ya Tube Babbar Riga Ya Tafi Kotu Kare El Rufa'i

  • Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa ya shiga tawagar lauyoyin da ke kare tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
  • Shari’ar ta shafi zargin kutse ba bisa ƙa’ida ba cikin tattaunawar wayar Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu
  • Dalung ya ce ya shiga tawagar ne domin bayar da gudummawarsa wajen kare haƙƙin kowane mutum na samun adalci da sauraron ƙarar da ake yi masa bisa doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon minista, Solomon Dalung ya sanar da shiga tawagar lauyoyin da ke kare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a shari’ar da ake yi masa kan zargin sauraren tattaunawar wayar Malam Nuhu Ribadu.

Dalung ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce El-Rufai ya halarci zaman kotu ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, domin fara kare kansa a shari’ar.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Barista Solomon Dalung
Solomon Dalung da wasu lauyoyi a kotu. Hoto: Solomon Dalung
Source: Facebook

Dalung ya wallafa a Facebook cewa ana sauraron ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya, Kotun Mai lamba 7 da ke Abuja, kan zargin kutse ba bisa ƙa’ida ba cikin tattaunawar wayar NSA.

Dalilin shigar Dalung shari'ar

Dalung ya ce shiga tawagar lauyoyin El-Rufai wata dama ce gare shi ta amfani da ƙwarewarsa a fannin shari’a wajen kare muhimmin ƙa’idar dimokuraɗiyya.

Ya bayyana cewa kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da matsayinsa, ra’ayinsa na siyasa ko shahararsa ba, yana da haƙƙin samun shari’a cikin adalci da kariyar doka.

A cewarsa, dole ne a gwada zarge-zarge da hujjoji, kuma duk wanda ake tuhuma ya kamata a ba shi damar kare kansa.

Dalung ya ce kotu ce wurin da ake gabatar da hujjoji da muhawara, sannan a bar doka ta yanke hukunci ba tare da son kai ko wariya ba.

Nasir El-Rufa'i
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Facebook

Kotu ta ƙi yarda da buƙatar El-Rufai

Kara karanta wannan

An kama mai shiga makabarta yana cire likkafani a jikin gawar da aka birne

A ranar 26 ga Oktoba, 2026, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da buƙatar El-Rufai ta cewa babu isassun hujjojin da za su sa ya kare kansa a shari’ar.

Sai dai hukuncin bai tabbatar da cewa El-Rufai ya aikata laifin da ake zarginsa da shi ba, illa dai ya nuna cewa akwai hujjojin da ya kamata ya amsa a gaban kotu.

A zaman kotun na ranar Laraba, El-Rufai ya fara gabatar da kare kan shi tare da musanta zargin sauraren tattaunawar wayar Ribadu ko umartar wani ya yi hakan.

Rahoton Blueprint ya bayyana cewa kotun ta ɗage ci gaba da sauraron kariyarsa zuwa ranakun 15 da 16 ga Fabrairu, 2027.

Yahaya Bello ya shawarci El-Rufa'i

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce yana da tabbacin kayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a zaɓen Majalisar Dattawa na 2027.

Bello ya kuma ce da ya samu damar tattaunawa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kafin fara shari’o’insa, da ya shawarce shi ya rage yawan magana.

Hakan na zuwa ne yayin da El-Rufai ke fuskantar shari’o’i a kotu, ciki har da ƙarar da ta shafi zargin kutse cikin tattaunawar wayar Malam Nuhu Ribadu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng