Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad sun samu 'karuwar da namiji

Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad sun samu 'karuwar da namiji

  • Allah ya azurta diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad da samun karuwar da namiji
  • Hanan ta haifi santalelen dan nata ne a kasar Turkiyya a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris
  • An sakawa sabon jinjirin suna Muhammad Zayd kamar yadda mahaifinsa ya bayyana

Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan tare da mijinta Muhammad Turad Sha’aban, sun samu karuwar da namiji a kasar Turkiyya.

Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa an haifin dan ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, Solacebase ta rahoto.

Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad sun samu 'karuwar da namiji
Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad sun samu 'karuwar da namiji Hoto: @arewafamilyweddings
Asali: Instagram

An kuma tattaro cewa daga uwar har dan suna nan cikin koshin lafiya.

Hakazalika shafin Instagram mai suna mr_mrs_arewa ya nakalto cewa Muhammad Turad ya sanar da labarin samun karuwar tasu a shafinsa, inda ya bayyana cewa sun sanya wa yaron suna Muhammad Zayd.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan bayan shafe kwanaki ana duba lafiyarsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Turad ya rubuta a shafin nasa:

“Allah ya azurta ni da matata da haihuwar da namiji! Alhamdulillah.
“Mun saka masa suna Muhammad Zayd (Hibbu Rasulallah)."

Idan za ku tuna, Hanan ta auri sahibin nata ne a watan Satumban 2020, a wani gagarumin shagali da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ke ce addu'a ta da aka karba: Hanan Buhari da Muhammad Turad sun shekara 1 da aure

A baya mun kawo cewa diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Hanan Buhari da mijin ta, Muhammad Turad Sha'aban sun yi murnar cikarsu shekara daya cif da aure a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba, 2021.

Hazikar mai daukar hoton tare da mijinta sun garzaya shafukansu na Instagram inda suka taya juna murnar cika shekara 1 da aure.

Kara karanta wannan

Bacin zuciya: Kotu ta yankewa malamin addini hukuncin kisa bayan ya kashe amininsa

"Ke ce addu'a ta da aka ansa! Ina mana murnar zagoyar ranar auren mu" Mohammed ya wallafa yayin da ya hada da kyakyawan hotonsu tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel