Yan adawa 5 da APC ta jawo aka sa a kwamitin neman tazarcen Tinubu
Abuja - Jam’iyyar APC ta fitar da sunayen mutanen da za su yi mata aikin tallar Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A cikin sabon kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar akwai fitattun ‘yan adawa wadanda ba ‘yan APC ba ne.
Rahotonmu ya yi kokarin kawo sunayen manyan ‘yan adawa da aka ga sun shiga cikin kwamitin yakin zaben APC.

Source: Facebook
'Yan adawa a kwamitin kamfen Bola Tinubu
1. Nyesom Wike
BBC ta yi bayanin yadda Nyesom Wike ya samu gurbi a hukumance cikin masu taya Bola Tinubu kamfe a 2027.
Duk da yana cikin ‘yan jam’iyyar PDP, an nada shi a matsayin jagoran kamfen APC a babban zabe a Rivers da Abuja.
Ministan na Abuja bai taba boye alakarsa da shugaba Tinubu ba tun a zaben 2023.
2. Charles Chukwuma Soludo
Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo yana cikin wadanda za su dage sai APC ta ci zaben shugaban kasa.
APC ta dauko gwamnan Anambra ya taya ta kamfe ba tare da la’akari da cewa shi ‘dan jam’iyyar adawa ta APGA ne ba.
Kafin sunan shi ya fito an ji yadda gwamnatinsa ta ke yakar takarar Peter Obi na NDC wanda ya yi gwamna kafin shi.
3. Ademola Adeleke
Premium Times ta ce bayan ya sha nanata cewa yana goyon bayan tazarcen Bola Tinubu, an tafi da Ademola Adeleke.
Gwamnan zai yi wa shugaban kasa aiki a Osun wannan karo bayan kokarin da ya yi wa Atiku Abubakar a 2023 a PDP.
Irinsu Adebisi Akande da Iyiola Omisore sun shiga kwamitin yakin neman zaben, amma babu sunan Gboyega Oyetola.
4. Ibrahim Hassan Dankwambo
Ibrahim Hassan Dankwambo wanda sanata ne mai-ci karkashin jam’iyyar PDP yana cikin masu yi wa APC kamfe.
Sanatan na Arewacin jihar Gombe yana cikin mashawarta a majalisar kamfen APC a babban zabe.
Watakila gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya wanda yake harin kujerar Dankwambo ba zai ji dadin ganin shi a kwamitin ba.
5. Segun Sowunmi
Wani ‘dan adawan da aka tsinta a kwamitin shi ne Segun Sowonmi wanda a baya aka san shi a gidan Atiku Abubakar.
The Guardian ta ce tsohon kakakin tsohon mataimakin shugaban kasar yana cikin kwamitin yada labarai na kamfen APC.
Zai yi aiki da irinsu Tunde Rahman, Sunday Dare, Daniel Bwala da Felix Morka duk da tsohon ubangidansa yana ADC.

Source: Facebook
An kyale gwamnan APC an dauko Wike
Yanayin siyasar Rivers dabam ce shi ya sa aka ga Nyesom Wike yana kula da yakin neman zaben Bola Tinubu.
Ministan ya musanta cewa an ware Gwamna Simi Fubara, yana mai cewa yana da gudunmawa da yake bayarwa.
Wike ya kara da cewa Fubara yana halartar tarurruka kuma yana kokarin rike jam’iyyar APC a jihar Rivers.
Asali: Legit.ng

