Gwamna Ya Ayyana Yaki da Yan Bindiga, Ya Kaddamar da Dakarun Tsaron Daji 1,000

Gwamna Ya Ayyana Yaki da Yan Bindiga, Ya Kaddamar da Dakarun Tsaron Daji 1,000

  • Gwamna Dauda Lawal ya halarci bikin yaye jami’an tsaron daji 1,000 da suka kammala daukar horo domin taimakawa wajen yaƙi da ’yan bindiga
  • Jami’an sun fito ne daga ƙananan hukumomi 13 na Zamfara, inda suka shafe watanni biyu suna samun horo
  • Gwamna isLawal ya ce gwamnatin tarayya za ta ɗauki nauyin alawus ɗinsu, yayin da jihar za ta samar musu da motoci, babura da sauran kayan aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya halarci bikin jami’an gadin daji 1,000 da suka kammala daukar hoto a ƙarƙashin shirin shugaban ƙasa na samar da jami’an tsaron daji.

An samar da wannan shiri ne domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga da dawo da tsaro a faɗin jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun raɗawa Atiku sabon suna gabanin zaben shugaban ƙasa na 2027

Dauda Lawal.
Gwamna Dauda Lawal a wurin kaddamar da jami'an tsaron daji a jihar Zamfara Hoto: Abdul Balarabe
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa dakarun sun fito ne daga ƙananan hukumomi 13 na jihar, inda suka shafe watanni biyu suna samun horo mai zurfi.

Ana sa ran za a tura su zuwa al’ummomi daban-daban a faɗin Zamfara domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamna Lawal ya shirya yaki da yan bindiga

Da yake jawabi a bikin kammala horon da aka gudanar a Gusau, Gwamna Lawal ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da ya bayar ga shirin.

Ya kuma gode wa masu horar da jami’an daga rundunar soji da kuma iyalan waɗanda suka samu horon bisa taimakon da suka bayar a lokacin horon.

Gwamnan ya buƙaci jami’an da su gudanar da ayyukansu bisa ƙa’idojin da doka ta tanada, su riƙa rubuta bayanan ayyukan da suka gudanar, su kai rahoto ga hukumomin da suka dace, sannan su mutunta tare da kare mutane.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta tabbatar da kashe mutum kusan 100 a jihar

Gwamnatin Zamfara za ta samar da kayan aiki

Lawal ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce za ta ɗauki nauyin biyan alawus ɗin jami’an, yayin da gwamnatin jihar za ta samar musu da motocin aiki, babura da sauran kayan aikin da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya ce:

“Gwamnatin tarayya ce ke da alhakin biyan alawus ɗinsu, yayin da gwamnatin jihar za ta samar da motoci, babura da sauran kayan aiki domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.”

Gwamnan ya nuna damuwa kan ci gaba da kai hare-hare kan al’umma, yana mai cewa zai yi duk abin da ya dace a matsayinsa na Babban Jami’in Tsaro na jihar domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Dauda Lawal.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal yana magana a wurin taro a Gusau Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Ya tuna cewa a baya ya yi kira ga ’yan bindiga da su ajiye makamansu domin gwamnati ta samar da makarantu, hanyoyi, ruwan sha da sauran abubuwan more rayuwa a yankunansu, amma suka ƙi amincewa.

Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga wata yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga ba, yana mai cewa babu wani dalilin yin hakan.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Ya kuma buƙaci jami’an tsaron da su kasance masu kishin ƙasa, tare da kare duk al’ummar da aka tura su aiki gwargwadon ƙarfinsu.

An ware N10m ga kowace mazaba

Gwamnan ya bayyana cewa kwanan nan ya bayar da umarnin cewa dukkan mazabu 147 da ke jihar Zamfara su zaɓi matasa da za a horar tare da ba su kayan aiki domin kare al’ummominsu.

Ya ce kowace mazaba za ta samu tallafin Naira miliyan 10 daga gwamnatin jihar Zamfara domin taimaka wa shirin.

Gwamna Lawal ya ce ba sulhu da yan bindiga

Kun ji cewa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada matsayarsa kan sulhu da yan bindiga, ya ba su zabi biyu na ajiye makamai ko su fuskNci hukunci.

Babban Sakataren Gwamnan, Mukhtar Musa, ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa jami'an tsaro da kayan aiki, alburusai da sauran buƙatun yaƙi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262