PDP Ta Shaida Matakin da Ake Dauka game da Cire Sunayen Pantami da Wasu ‘Yan Takara

PDP Ta Shaida Matakin da Ake Dauka game da Cire Sunayen Pantami da Wasu ‘Yan Takara

  • Jam’iyyar PDP ba za ta zura ido tana kallon ikon Allah bayan cire mata ‘yan takaran gwamna a wasu jihohi ba
  • Kakakin jam’iyyar a Najeriya ya fitar da jawabi yana mai tabbatar da cewa suna tattaunawa da hukumar INEC
  • Jungudo Mohammed ya yi kira ga masu neman takara da magoya bayansu su guji abin da zai jawo matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - PDP ta fara tattaunawa da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin warware batun hana wasu takara.

An samu matsalar cire sunayen wasu ’yan takarar PDP daga jerin sunayen masu neman gwamna a 2027 da hukumar ta fitar.

Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami da wasu manya wajen jana'izar Nafiu Baba Ahmed a Abuja Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Jam'iyyar PDP tana magana da INEC kan takara

Punch ta ce an bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na kasa, Jungudo Mohammed, ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce jam’iyyar na daukar lamarin da muhimmancin da ya dace, kuma tana neman warware matsalar cikin lumana bisa ka’ida.

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

Jam’iyyar adawar ta kuma bukaci ’yan takarar da abin ya shafa, mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu.

Jungudo Mohammed ya kuma yi kira da su yi hajuri yayin da ake ci gaba da tattaunawa da INEC.

Sanarwar ta ce:

“Jam’iyyar na son tabbatar wa dukkan ’yan takarar da abin ya shafa, mambobinta da magoya bayanta cewa tuni ta fara tattaunawa da INEC domin magance matsalolin da suka jawo cire sunayen, da nufin cimma matsaya cikin lumana bisa doka da ka’idojin zabe.”

Kiran da PDP ta yi wa masu takara da masoya

PDP ta kara da cewa tana daukar lamarin da matukar muhimmanci, kuma za ta sanar da jama’a duk wani sabon bayani da ya taso.

Ta kuma jaddada aniyarta ta tabbatar da cewa an magance dukkan korafe-korafen da suka dace tare da hukumar zaben na kasa.

Saboda haka, jam’iyyar ta bukaci duk wadanda abin ya shafa da su guji duk wani mataki ko furuci da ka iya kawo matsala da INEC.

Jaridar This Day ta tabbatar da tattaunawar da jam’iyyar PDP ta ke yi da hukumar zabe a wannan gaba.

Kara karanta wannan

Kano: NDC ta yi mamakin cire sunan Gwarzo, ta faɗi tabbacin da INEC ta ba ta

Manyan wadanda aka hana su takara a PDP

Cikin wadanda ba a ga sunayensu ba akwai Ladi Adebutu da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami.

Farfesa Isa Pantami, shi ne wanda ya lashe zaben zama dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Gombe.

Cire sunan shi ya biyo bayan takaddamar shari’a kan zaben fitar da gwani da ya samar da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar adawar.

A cewar rahotanni, cire sunan Adebutu shi kuma yana da alaka da rashin sunansa a rajistar mambobin PDP da aka mika wa hukumar INEC.

Sai dai bangaren jam’iyyar PDP na Ogun ya karyata zarge-zargen, yana mai cewa Adebutu cikakken ‘da ne da ya bi ka’idojin yin rajista.

Pantami
Isa Ali Pantami a fadar Sarkin Kaltungo domin yi masa ta’aziyya a Gombe Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Isa Pantami ya yi maganar rasa takara

Da INEC ta cire sunan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami daga cikin jerin sunayen yan takarar gwamna a jihar Gombe, an ji labari ya fitar da jawabi.

Kara karanta wannan

'Ba a cire sunan Pantami a takara ba': PDP ta kwantar wa masoyanta hankali

Bangaren Pantami ya bayyana cewa tawagar lauyoyinsu na tattaunawa da hukumomin domin warware matsalar cikin wa'adin da aka ba da.

'Dan takaran ya karfafa wa magoya baya da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da kasancewa masu kyakkyawan fata da hadin kai a Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng