Yadda ake Barazanar Kashe Shugaban INEC kan Zaben 2027 a Kullum

Yadda ake Barazanar Kashe Shugaban INEC kan Zaben 2027 a Kullum

  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce yana samun saƙonnin barazanar kashe shi kusan kullum saboda aikinsa na jagorantar hukumar zaɓe
  • Ya bayyana aikin INEC a matsayin wanda ba a yaba wa mai yinsa, inda ya ce jami’an hukumar na fuskantar cin zarafi da matsin lamba daga ɓangarori daban-daban
  • Amupitan ya gargaɗi kwamishinonin zaɓe da su guji sakaci yayin shirye-shiryen zaɓen 2027, yana mai cewa hukumar ba ta da damar yin kuskure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa yana fuskantar barazanar kashe shi kusan kullum saboda aikin da yake yi na jagorantar hukumar.

Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin wani taron shawarwari da kwamishinonin zaɓe na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).

Kara karanta wannan

Tinubu ka iya rasa muhimmiya jiha a Arewa kan rigimar gwamna da manyan kasa

Joash Amupitan
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Arise ta rahoto ya ce hukumar na fuskantar hare-hare da barazana daga wasu ɓangarori da ke ƙoƙarin tsoratar da jami’anta, amma ya buƙaci ma’aikatan INEC kada su bari hakan ya ɗauke hankalinsu.

Ana yi wa Amupitan barazana

Shugaban INEC ya bayyana cewa yana samun saƙonnin barazanar kisa a kusan kowace rana, lamarin da ya ce wani lokaci kan sa shi tambayar ko ya dace a riƙa fuskantar irin wannan matsin lamba.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce duk wanda ke tunanin cewa yana lalata INEC, a zahiri yana lalata dimokuraɗiyyar Najeriya ne.

Amupitan ya koka kan yadda jami’an hukumar ke fuskantar suka da cin zarafi duk da ƙoƙarin da suke yi wajen gudanar da ayyukansu.

Ya bayyana cewa aikin hukumar zaɓe tamkar aikin da ba a gode wa mai yinsa ba ne, domin komai ƙoƙarin mutum, ana ci gaba da sanya shi a ido tare da zagin shi a wasu lokuta.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Maganar Abba ta jawo ana so Tinubu ya sauka ko a tsige shi

Ya kuma ce yana da tabbacin cewa wasu kwamishinonin zaɓe na fuskantar irin waɗannan barazanar daga ƙungiyoyi daban-daban da ke ƙoƙarin tsoratar da su.

An gargaɗi jami’an INEC

Farfesa Amupitan ya gargaɗi kwamishinonin zaɓe da su guji sakaci ko gazawa wajen gudanar da ayyukansu yayin babban zaɓen 2027.

Ya ce INEC ta shiga wani muhimmin mataki na shirye-shiryen zaɓen, don haka lokaci bai ƙara ba wa hukumar damar dogon zama wajen tattaunawa ba tare da aiwatar da tsare-tsare ba.

Jami'an hukumar INEC
Joash Amupitan da wasu jami'an INEC. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

A cewarsa, dole ne a tabbatar da cewa dukkan shirye-shiryen da aka tsara a hedikwatar hukumar sun zama ayyuka na zahiri cikin tsari da ƙwarewa a jihohi, ƙananan hukumomi da mazabu.

Ya jaddada cewa kwamishinonin zaɓe su ne manyan jami’an da ke jagorantar ayyukan INEC a jihohinsu, don haka suna da babban nauyin tabbatar da nasarar zaɓe.

Za yi zaben gwaji

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta zaɓi rumfunan zaɓe 17,676 a faɗin Najeriya domin gudanar da gwajin na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Hukumar ta bayyana cewa za a gudanar da gwajin ne a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026, daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana.

Za a gudanar da gwajin a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaba, a mazabu 8,838 da ke faɗin ƙasar nan, gabanin babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng