Wike Ya Yi Gaban Kai, Ya Ba Kan Shi Sarkin Yakin Zaben Tinubu a Abuja da Rivers

Wike Ya Yi Gaban Kai, Ya Ba Kan Shi Sarkin Yakin Zaben Tinubu a Abuja da Rivers

  • Nyesom Wike ya ayyana kansa a matsayin jagoran yakin neman sake zaben Bola Tinubu a Abuja a 2027
  • Ya hada kan wasu mambobin APC da PDP da zau su taimaka wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa
  • Wike ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen sun kawo wa Abuja cigaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya kara dage wa wajen yi wa Bola Tinubu kamfe a Najeriya.

Nyesom Wike ya ayyana kansa a matsayin wanda zai jagoranci ayyukan yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu a Abuja a 2027.

Ministan Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike tare da Bola Tinubu Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Nyesom Wike ya zama shugaban kamfen Bola Tinubu

Rahoton Punch ya ce Wike ya kuma yi alkawarin tsara yadda za a gudanar da yakin neman zaben a Abuja da kuma jihar Rivers.

Ministan birnin tarayyan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na Rainbow Coalition a Abuja.

Kara karanta wannan

Amaechi zai iya samu kan shi a matsala saboda kalaman da ya yi game da APC

A taron, Wike ya bayyana shirin hadin gwiwar siyasa da ya kunshi ‘yan jam'iyyun APC da na PDP mai adawa a zabe mai zuwa.

Wike ya ce za su hada kai domin ganin Mai girma Bola Tinubu ya sake lashe zaben da za a yi.

'Yan takaran majlisa a PDP sun janye wa APC

Haka kuma, wasu 'yan takarar PDP na Majalisar Dokokin Tarayya sun bayyana goyon bayansu ga takwarorinsu na APC mai mulki.

Wike ya ce sun amince su hada kai wajen tallafa wa Tinubu da kuma tabbatar da nasarar 'yan takarar APC a zaben ‘yan majalisar tarayya.

Ya ce:

“Dangane da zaben shugaban kasa, dukkanmu mun amince da Bola Ahmed Tinubu. Zan jagoranci ayyukanmu a Abuja da jihar Rivers. Wannan ya nuna muhimmancin aikin da ke gaba na.”

Ya kara da cewa shi ne zai jagoranci ayyukan yakin neman zabe a birnin Abuja.

Wike ya hada-kan 'yan PDP da APC a Abuja

Taron ya samu halartar shugabannin APC da PDP, sanatoci na yanzu da na baya, 'yan takarar majalisar dokoki da shugabannin Abuja.

Kara karanta wannan

Wike ya bayyana mutumin da ya yi silar hawan shi kujerar gwamna a Rivers

This Day ta ce Wike wanda asalinsa ‘dan jam’iyyar PDP ne ya bukaci mahalarta taron su ajiye bambancin jam'iyyunsu a gefe guda a 2027.

Tsohon gwamnan yake cewa hadin kansu zai taimaka wajen cimma burinsu a zaben da za a yi a shekarar 2027.

Ya kawo zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a 2024 a matsayin misali na yadda hadin kan 'yan siyasa zai iya sauya sakamakon zabe.

A cewarsa, hadin gwiwar wasu ‘yan APC da PDP ya taimaka wajen hana gwamnan jihar na lokacin sanya wanda yake so ya gaje shi.

Sai dai Wike ya bayyana cewa babban abin da kawancensu ya maida hankali a kai shi ne zaben shugaban kasa da ya nada shi minista.

Ya ce kowace jam'iyya za ta yanke matsayinta kan sauran zabukan da za a shiga a badi.

Mene ne dalilin Wike na goyon bayan Tinubu?

Wike ya nemi a nuna masa karamar hukumar Abuja da ba ta amfana da ayyukan raya kasa da sauye-sauyen da Tinubu ya kawo ba.

Ya ambaci kafa Hukumar Kula da Ma'aikatan Gwamnatin Abuja, nada shugaban ma'aikata daga ma'aikatan yankin a cikin romon da aka samu.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Tunanin Tinubu ya mamaye zuciyar minista, yana zuwa har a cikin barci

Ministan ya kuma lissafa gine-gine da gyaran hanyoyi, gyaran makarantu, ofisoshin 'yan sanda da sauran ayyukan more rayuwa a Abuja.

Sai Bola Ahmed Tinubu/Uba Sani a Kaduna

An samu labari cewa Dr. Aminu-Zaria ya ce Bola Tinubu da Uba Sani sun cancanci tazarce saboda ayyukan da suka fara a Kaduna da Najeriya.

Kungiyarsa ta Tinubu/Uba Sani Mobilisation Network na shirin samar wa APC ƙuri’u miliyan 1.2 a jihar Kaduna a zaben da za a yi a badi.

Aminu-Zaria ya bukaci al’ummar Kaduna su ajiye son zuciya a gefe, su duba ayyukansu, su zabi APC a 2023 domin a karasa ayyukan da aka fara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng