Tinubu Ya Tuna da Iyalan Sojojin da Suka Mutu a Hatsarin Jirgi, Ya ba Su Abin Duniya
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da bai wa iyalan jami’an soji da fararen hula 25 da suka mutu a hatsarin jirgin NAF gidaje masu
- Tinubu ya kuma amince da bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga iyalan wadanda suka rasu a hatsarin jirgin saman da ya faru ranar 5 ga Oktoba, 2026
- Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin bikin tunawa da wadanda suka mutu, inda ya ce Najeriya za ta samar wa iyalansu gidaje domin karrama sadaukarwar da suka yi wa kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi abin a yaba ga jami'an sojoji da fararen hula da suka yi hatsarin jirgi.
Shugaban ya amince da bai wa iyalan mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya (NAF) gidaje masu dakuna uku a Abuja.
Tinubu ya kuma amince da bayar da Naira miliyan 100 a matsayin tallafin gwamnatin tarayya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin, cewar Punch.
Shugaban kasar ya bayyana wadannan matakai ne a ranar Alhamis yayin bikin tunawa da wadanda suka mutu da kuma shimfida furanni domin karrama mutane 25 da suka rasu a hatsarin jirgin NAF ATR 42.
Ya ce rabon gidajen wata hanya ce ta nuna godiya da karramawa ga jami’an soji da sauran mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin ranar 5 ga Oktoban 2026.
A cewar Tinubu:
“A matsayin wata muhimmiyar alama ta nuna godiyar kasa, na amince da ware gidaje masu dakuna uku a karkashin shirin Renewed Hope Housing Project da ke Abuja ga iyalan kowane jami’in soji da ya rasa ransa a wannan hatsari.
“Babu wani gida da zai iya maye gurbin wanda kuka rasa, amma sun sadaukar da rayukansu saboda Najeriya, kuma Najeriya za ta samar wa iyalansu gida.”
Tinubu ya kara da cewa wannan tallafi ba zai takaita ga iyalan jami’an soji kadai ba, domin za a kuma bai wa iyalan fararen hular da ke cikin jirgin tallafin gidajen.
Ƙarin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng
