Jigo a ADC Ya Ce an Samu Kiran Waya daga Kabarin Buhari kan Wanda Za a Zaba a 2027

Jigo a ADC Ya Ce an Samu Kiran Waya daga Kabarin Buhari kan Wanda Za a Zaba a 2027

  • Solomon Dalung ya yi zargin cewa Aisha Buhari ta ziyarci Atiku domin sanar da shi cewa an miƙa masa kuri’u miliyan 12 na marigayi Muhammadu Buhari
  • Dalung ya yi ikirarin ne a wata hira da wani bababn gidan talabijin a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamban shekarar 2027
  • Atiku ya taɓa bayyana cewa Aisha Buhari ta ziyarce shi a gidansa, sannan ta sake ganawa da shi a Saudiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Solomon Dalung, ya yi magana kan ziyarar da tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta kai wa Alhaji Atiku Abubakar.

Solomon Dalung ya yi zargin cewa tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta ziyarci Atiku Abubakar domin sanar da shi cewa an miƙa masa kuri’u miliyan 12 na marigayi Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Amaechi ya bar gwamnatin Atiku idan suka hau mulki

Aisha Buhari ta ziyarci Atiku
Aisha Buhari tare da Atiku yayin ziyarar da ta kai masa Hoto: @atiku
Source: Twitter

Dalung ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, yayin da ake tattauna batutuwan da suka shafi siyasar zaɓen 2027.

Ya kuma yi magana kan abin da ya kira kiran waya daga kabarin Buhari, inda ya yi ikirarin cewa marigayi shugaban ƙasar ya bukaci ’yan Najeriya su kaɗa ƙuri’unsu ga Atiku.

Sai dai waɗannan kalamai na Dalung ne, kuma bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da cewa an miƙa wa Atiku kuri’un ko kuma an yi irin wannan kira daga kabarin marigayin.

Ziyarar Aisha Buhari ga Atiku

Zargin Dalung ya ta’allaka ne kan wasu ganawa da aka sani tsakanin Atiku da tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar.

A watan Satumba, Atiku ya bayyana a bainar jama’a cewa ya karɓi bakuncin Aisha Buhari a gidansa.

Haka kuma, a watan Fabrairu, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce Aisha ta ziyarce shi a inda yake zaune a Saudiyya, tare da ɗiyarta.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: "Hukuncin kotu bai rusa takarar Atiku a 2027 ba"

Dalung ya bayyana waɗannan ziyarce-ziyarce a matsayin abubuwan da ke da alaƙa da siyasa, inda ya nuna cewa suna cikin wani yunƙuri na haɗa magoya bayan marigayi Buhari domin su mara wa Atiku baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku a matsayin ɗan takarar ADC

Atiku Abubakar ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a babban zaɓen 2027, bayan ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar.

Haka kuma, kwamitin zartarwa na ƙasa na jam’iyyar, wato National Executive Committee (NEC), ya amince da takararsa.

Zargin da Dalung ya yi ya zo ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng