'Ba Mu Yi': APC Ta Gano Masu Saka Ƴan Daba Su Yi wa Tinubu Rashin Kunya
- APC ta zargi jam’iyyun ADC da NDC da daukar nauyin ’yan daba domin haddasa tarzoma a tarukan yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu
- Dele Alake ya ce ’yan adawa ne suka shirya harin da aka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa a Abuja ranar Juma’a
- APC ta kuma zargi ’yan adawa da lalata allunan tallan jam’iyyar tare da barazana ga magoya bayanta a yankin Kudu maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyun adawa na ADC da NDC da daukar nauyin ’yan daba yayin kamfen dinta.
Jam'iyyar ta ce suna yin hakan ne domin tarwatsa tarukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar mai mulki.

Source: Facebook
APC ta zargi ADC da NDC kan siyasa
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Dele Alake, ne ya yi wannan zargi cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan
2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa
Alake ya yi zargin cewa harin da aka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa a Abuja ranar Juma’a, an shirya shi ne da taimakon jam’iyyun adawa.
Ya kuma yaba wa jami’an tsaro bisa yadda suka nuna dattako da kauce wa duk wani abu da zai iya haddasa rikici yayin faruwar lamarin.
Haka kuma, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa umarnin da ya bayar na sakin mutanen da aka kama dangane da harin.
APC ta yi gargadi kafin fara kamfen zabe
Alake ya ce tun sa'o'i kafin fara gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Kaduna ranar 24 ga Oktoba, 2026, suka sanar da ’yan Najeriya game da wani shiri na haddasa tashin hankali.
Ya ce sun sanar da jama’a cewa jam’iyyun ADC da NDC sun tsara amfani da hotunan bogi da fasahar AI, labaran ƙarya, zanga-zangar da aka dauki nauyi da sauran dabarun farfaganda.
A cewarsa, manufar wannan shiri ita ce karkatar da ra’ayin jama’a da yada bayanan ƙarya game da Najeriya, Shugaba Tinubu, APC da shirye-shiryen babban zaɓen shekara mai zuwa.
Alake ya yi zargin cewa waɗannan tsare-tsare sun fara bayyana, inda ya ce manufarsu ita ce yaudarar ’yan Najeriya da ƙasashen duniya ta hanyar nuna cewa jama’a ba sa goyon bayan shugaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa ADC da NDC suna daukar nauyin ’yan daba tarrme da ba su sanduna da alluna domin zuwa tarukan APC suna rera taken ‘Ba mu yi’.
Ya ce abin da ya faru a masallacin Abuja ranar Juma’ar da ta gabata shi ne sabon misalin wannan batu, inda ya zargi wasu ’yan daba da jifan ayarin motocin shugaban ƙasa da duwatsu.
APC ta yaba wa jami’an tsaro da Tinubu
Alake ya yabawa jami’an tsaron da ke tare da ayarin motocin shugaban ƙasa bisa nuna kwarewa da hakuri a lokacin da lamarin ya faru.
Ya kuma yaba wa Tinubu bisa umarnin sakin mutanen da aka tsare, yana mai cewa shugaban ƙasar ya nuna halin dattako.
Zargin barazana ga magoya bayan APC
Haka kuma, Alake ya ce kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC na nuna damuwa kan zargin cin zarafi da ake yi wa wasu mambobinta da magoya bayanta a Kudu maso Gabas.
Ya yi zargin cewa ana yi musu barazana tare da lakaba musu sunan masu cin amana saboda kin goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi.
Bugu da ƙari, ya yi zargin cewa wasu mutanen da ke samun goyon bayan ’yan adawa na lalata allunan tallan yaƙin neman zaɓen APC da daddare.
Ya ce irin waɗannan ayyuka ba su dace da tsarin dimokuraɗiyya ba, yana mai jaddada cewa APC na goyon bayan zaɓe cikin lumana, gaskiya da adalci.
Alake ya ce bai kamata a tauye damar kowace jam’iyya ko ɗan takara na gudanar da harkokin siyasa a ko’ina cikin ƙasar ba.
A ƙarshe, ya yi kira ga shugabannin ADC da NDC da su dakatar da shigar da matasa cikin ayyukan siyasa masu haɗari da ka iya jefa rayuwarsu cikin barazana.
Ya zarge su da amfani da matasa wajen irin waɗannan ayyuka, alhali kuwa ’ya’yansu suna rayuwa cikin jin daɗi a ƙasashen waje.
Ƙarin bayani a tafe......
Asali: Legit.ng

