"Na Shirya": Uba Sani Ya Bayyana Kololuwar Shirinsa kan Kare Tazarcen Tinubu
- Uba Sani ya ce ba zai yi nadamar goyon bayan Tinubu ba, kuma zai ci gaba da mara masa baya har zuwa ƙarshen lokacin yaƙin neman zaɓe
- Gwamnan ya danganta goyon bayansa ga alaƙar siyasa da ke tsakaninsu tun shekarar 1994, lokacin gwagwarmayar dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya
- Ya ce amincewa da wasu manyan ayyukan jami'o'i da gyaran hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari na daga cikin abubuwan da suka amfani jihar a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana shirinsa na ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake zaɓensa a babban zaɓen 2027.
Gwamnan ya ce yana goyon bayan Tinubu ne saboda gamsuwa da manufofinsa, duk da rashin jin daɗin da wasu 'yan Najeriya ke nunawa kan tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki.

Source: Twitter
Uba Sani ba zai yi nadama ba
Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Daily Politics na tashar Trust TV ranar Talata, 27 ga watan Oktoban 2026.
“Ba ni da dalilin neman afuwa saboda goyon bayan Bola Ahmed Tinubu, kuma zan ci gaba da goyon bayansa har zuwa minti na ƙarshe,” in ji gwamnan.
Da aka tambaye shi ko a shirye yake ya fuskanci babban haɗarin siyasa saboda Tinubu, Uba Sani ya ce yana da tabbacin lokaci zai tabbatar da cewa matsayarsa daidai ne.
“Zan iya gaya maka a yau, gobe da kuma jibi cewa za a tabbatar da gaskiyar matsayina,” in ji shi.
Ya tuna alaƙarsa da Tinubu
Gwamnan ya ce ɗaya daga cikin dalilan goyon bayansa ga Tinubu shi ne doguwar alaƙar da ke tsakaninsu, wadda ta samo asali tun shekarar 1994.
Ya bayyana cewa a wancan lokaci, suna cikin mutanen da suka yi gwagwarmayar dawo da mulkin dimokuraɗiyya bayan mulkin soja a Najeriya.
Uba Sani ya tuna cewa Tinubu, wanda ya yi alaƙa da ƙungiyar National Democratic Coalition (NADECO), ya tallafa wa masu fafutukar dimokuraɗiyya duk da haɗarin da ke tattare da gwagwarmayar.
A cewarsa, barazanar da ake fuskanta a lokacin ta sa wasu daga cikin masu fafutukar barin ƙasar domin tsira da rayukansu.
Gwamnan ya ce irin wannan tarihin gwagwarmaya da kuma burinsu na ƙara rarraba iko tsakanin matakan gwamnati sun taimaka wajen tsara yadda yake kallon shugabancin Tinubu.
Ya lissafa ayyukan da suka amfani Kaduna
Gwamna Uba Sani ya kuma ambaci wasu ayyuka da matakan gwamnatin tarayya da ya ce sun amfani Jihar Kaduna tun bayan hawan Tinubu kan mulki.
Daga ciki akwai amincewa da wasu tsare-tsaren kafa jami'o'in gwamnatin tarayya guda huɗu da kuma aikin sake gina hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Jami'o'in da ya lissafa sun haɗa da Federal University of Applied Sciences da ke Kudancin Kaduna, Federal University of Education a Zariya, da Federal University of Petroleum Resources da ake shirin kafawa a Rigachikun.
Ya kuma ambaci shirin mayar da Kaduna Polytechnic zuwa jami'ar fasaha ta gwamnatin tarayya.
Gwamnan ya jaddada cewa waɗannan ayyuka ba wata alfarma ce da aka yi masa da kansa ba, illa dai amfanin da aka kawo wa al'ummar jihar.
“Alfamar da ya yi ba gare ni ba ce, domin bai ba ni wani abu na kaina ba. Jihar ce ta amfana,” in ji Uba Sani.
Ya kuma nuna cewa naɗa wasu 'yan asalin Kaduna a manyan muƙaman gwamnatin tarayya na daga cikin abubuwan da yake ganin sun nuna yadda jihar ke samun wakilci a gwamnatin Tinubu.

Source: Facebook
Tinubu ya je Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai girma Bola Tinubu ya je Kaduna domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a hukumance gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
An tsara kaddamar da yakin neman sake zaben Tinubu/Shettima a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, 2026.
Asali: Legit.ng


