An Fara Zuwa Kamfen da Bindiga, INEC Ta Yi Gargadi kan Zubar da Jini

An Fara Zuwa Kamfen da Bindiga, INEC Ta Yi Gargadi kan Zubar da Jini

  • Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta gargadi ’yan siyasa cewa burinsu na neman mulki bai kai darajar jinin ko da mutum daya daga cikin ’yan Najeriya ba
  • Hukumar ta yi alkawarin daukar matakin kamawa, hukunta da gurfanar da jam’iyyu, ’yan takara da wakilai da aka samu da hannu wajen tashin hankali ko kalaman kiyayya
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi wannan gargadin ne a wani taron horaswa na musamman ga editoci da Kungiyar Editocin Najeriya ta shirya tare da hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – INEC ta gargadi ’yan siyasa da su guji duk wani mataki da zai iya jefa rayukan ’yan Najeriya cikin hadari yayin shirye-shiryen babban zaben 2027.

Farfesa Amupitan ya ce hukumar ba za ta bari gasar siyasa ta rikide zuwa tashin hankali, tsoratarwa ko yada kalaman da za su haddasa kiyayya ba.

Kara karanta wannan

An zo wajen: INEC za ta fadi makomar takarar Pantami da wasu 'yan siyasa

Joash Amupitan a ofishin hukumar INEC
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

INEC ba za ta zuba ido ba

Vanguard ta wallafa cewa Amupitan ya ce INEC ta kafa tsarin bibiyar abubuwan da ke faruwa domin gano tashin hankalin siyasa, daba da kalaman da za su iya jefa al’umma cikin hatsari.

Ya ce ta hannun Kwamitin Hadin Gwiwa Kan Tsaron Zabe, ICCES, hukumar ta kunna tsarin gargadi da wuri domin tattara bayanan tashin hankali da ake dangantawa da harkokin siyasa.

Ya ce duk jam’iyya ko dan takarar da aka samu da hannu wajen tunzura mutane zuwa tashin hankali, hana taron abokan hamayya ko amfani da ’yan daba dauke da makamai, zai fuskanci hukunci da kuma gurfanarwa.

“Babu wani mukamin siyasa a wannan kasa da ya kai darajar jinin ko da mutum daya daga cikin ’yan Najeriya,”

In ji shi.

Batun kamfen da bindiga

Amupitan ya kuma bayyana cewa jim kadan kafin ya fara jawabin nasa, an nuna masa wani bidiyo da ya ce ya yi kama da irin halayen da yake gargadi a kansu.

Kara karanta wannan

Saura kwana 100 zabe: INEC za ta yi wa 'yan Najeriya bayani kan takarar 2027

Ya ce an nuna masa wani dan takarar NDC a jihar Kano yana yakin neman zabe dauke da bindiga a hannunsa.

Ya kuma ce an samu wani mutum da ke barazanar amfani da AK-47 wajen kashe jami’an hukumar.

Shugaban INEC ya yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su yi taka-tsantsan, yana mai cewa zabe wani tsari ne na lokaci-lokaci da ake gudanarwa domin zabar shugabanni duk bayan shekaru hudu.

Wajen da ake kada kuri'a
Jami'an INEC na kirga kuri'u. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Korafi kan sayen kuri’u

Dangane da sayen kuri’u, Punch ta wallafa cewa shugaban INEC ya ce hukumar za ta dauki tsauraran matakai kan duk wani nau’in siyasar kudi kafin zaben 2027.

Ya ce mutuncin akwatin zabe yana fuskantar barazana idan aka mayar da kuri’ar dan kasa wata haja da ake saye da kudi.

Amupitan ya bayyana cewa INEC na aiki tare da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, Hukumar EFCC, Hukumar ICPC da NFIU, wajen dakile sayen kuri’u da sauran matsalolin kudi a zabe.

An gayyaci dan siyasar Kano

A wani labarin, kun ji cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta gayyaci Aminu Abdullahi Warkal domin yi masa tambayoyi kan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Tinubu ko Atiku: An yi hasashen wanda zai lashe zaben 2027 daga Turai

A cewar rundunar, an ga Warkal yana nuna wani makami da ake zargin bindigar pump-action ce yayin wani taron siyasa.

Kakakin ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce idan bincike ya tabbatar da zargin, hakan na iya zama saba wa dokar makamai tare da jefa tsoro da barazana ga zaman lafiyar jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng