‘Dan Takara Bai Rike Sirri ba, Ya Fadi Tanadin da ‘Yan Adawa Suke Yi wa Shugaba Tinubu

‘Dan Takara Bai Rike Sirri ba, Ya Fadi Tanadin da ‘Yan Adawa Suke Yi wa Shugaba Tinubu

  • Seyi Makinde, ya tabbatar da cewa shugabannin jam'iyyun adawa na ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar haɗa kai domin ƙalubalantar APC
  • Gwamnan Jihar Oyo ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ko Peter Obi da yake NDC
  • Ya ce ba a yanke shawarar wanda ya kamata ya zama ɗan takarar haɗakar ba tukuna, domin za a duba abubuwa da yawa kafin cin ma matsaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Oyo - Seyi Makinde, ya bayyana cewa ‘yan adawa suna tattauna wa domin tsaida ɗan takara guda zaɓen shugaban ƙasa da za a yi a 2027.

Don haka bai ƙi ya yi aiki tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ko Peter Obi domin ƙalubalanci jam'iyyar APC ba.

Gwamnan Jihar Oyo ya ce manyan 'yan siyasa da ke adawa suna duba yadda za su ga bayan Bola Ahmed Tinubu a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

"Alaƙa tsakanin Tinubu da gwamna ta yi tsami saboda neman takarar shugaban ƙasa a 2027"

Da yake magana a wata hira da ya yi da Ojy Okpe gwamnan ya yi watsi da batun cewa a shirye yake da ya haɗa kai da saura ‘yan adawa.

Ɗan takaran shugaban ƙasar na SDP ya nuna zancen ya wuce nan, ya ce yanzu haka tattaunawa ake yi dumu-dumu don a dunƙule wuri guda.

"Har yanzu muna kan tattaunawa
"Ba wai kawai ina maraba da hakan ba ne, a'a, muna tattaunawa sosai a kai."

- Seyi Makinde.

Wa 'yan adawa za su tsaida a 2027?

Sai dai ya ƙi bayyana wanda yake ganin ya fi dacewa a tsayar a matsayin ɗan takarar haɗakar, tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi.

Ya ce ya kamata 'yan adawa su yi amfani da hujjoji wajen yanke shawara, ciki har da manufofin 'yan takara da ayyukan da suka yi a baya.

Seyi Makinde ya kuma ce akwai buƙatar la’akari da ra'ayin jama'a, maimakon dogaro da son zuciya.

Ya ce:

"Za mu zauna mu duba tarihin ayyukan da aka gudanar a baya. Haka kuma za mu yi la'akari da ra'ayin jama'a. Duk waɗannan abubuwa ne za su haɗu wajen taimaka mana mu cimma matsaya."

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan sanda suka garkame Farfesa Zulum saboda ya nemi tsayawa takara a Borno

An ji Makinde ya fada wa Ojy Okpe cewa bambancin muradun 'yan siyasa ba yana nufin ba za su iya yin aiki tare ba, za su iya ajiye ra'ayinsu a gefe.

"Dangane da abin da za mu gani tsakanin yanzu da lokacin zaɓe, muna iya zama abokan hamayya, muna iya zama abokan haɗin gwiwa, ko kuma ɗaya daga cikinmu ya zama wanda ɗayan zai yi wa aiki."

- In ji 'dan takaran

Seyi Makinde zai iya aiki da Atiku Abubakar?

Makinde ya ce a shirye yake ya yi aiki da Atiku Abubakar wanda ake sa ran zai yi wa ADC takara, jaridar Tribune ta zo da labarin a ranar Juma’a.

Idan tsohon mataimakin shugaban ƙasar ne ya fi dacewa a tsayar a matsayin ɗan takarar da 'yan adawa za su mara wa baya, ya ce zai goyi bayan shi.

Makinde ya ce:

"A shirye nake in yi aiki tare da kowane ɗan Najeriya."

Lokacin da Okpe ta tambaye shi ko yana shirye a haɗa kai da wasu domin cimma burinsa na sake fasalin Najeriya, Makinde ya amsa da cewa:

Kara karanta wannan

"Yadda Tinubu zai nuna wa Atiku ƙarfin siyasa, ya lashe zabe a jihohi 36 a 2027"

"Domin sake fasalin Najeriya, eh."

A hirar ya kawo misalin zaɓen shugaban ƙasa na 1999, lokacin da Olu Falae ya samu gagarumin goyon baya a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Duk da yadda Yarbawa suka bi bayan shi, bai iya doke Olusegun Obasanjo na jam’iyyar PDP ba.

2027:‘Yar takarar NDC ta bar jam'iyya

A makon nan rahoto ya zo cewa Stella Charles Archibong ta koma goyon bayan APC da ta fice daga zaben gwamnan Cross River bayan samun takara.

’Yar takarar mataimakiyar gwamnan NDC ta fice daga jam’iyyar adawar, ta koma goyon bayan APC ta zarce, lamarin da ya ba masu bibiyar siyasa mamaki.

Stella Charles Archibong ta yi wa NDC godiya da aka tsaida ta tun farko a matsayin wanda za ta yi wa jam'iyyar takarar mataimakiyar gwamna a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng