Wata Mai Bukata Ta Musamman Ta Nunawa Duniya Cikinta, Ta Haifi Santalelen Yaro

Wata Mai Bukata Ta Musamman Ta Nunawa Duniya Cikinta, Ta Haifi Santalelen Yaro

  • Wata mata mai bukata ta musamman ta haidi santalelen danta, sannan ta nunawa duniya shi a wani bidiyo
  • A cikin bidiyon da Nikki Kademaunga ta wallafa a TikTok, mahaifiyar ta fara nunawa mutane lokacin da take dauke da juna biyu
  • Sannan ta bi shi da labari mai dadi na haihuwar dan nata sannan mutane suka dungi aika mata da sakon taya murna

Wata mata mai bukata ta musamman ta burge mutane a TikTok bayan ta wallafa wani bidiyo na lokacin da take dauke da juna biyu.

Matar ta haihu sannan ta wallafa bidiyon dan nata don murnar gagarumin kyautar da ta samu.

Mai bukata ta musamman ta haifi santalelen yaro
Wata Mai Bukata Ta Musamman Ta Nunawa Duniya Cikinta, Ta Haifi Santalelen Yaro Hoto: TikTok/@nikkikademaunga.
Asali: TikTok

Matashiyar bata da hannaye, kuma kafafuwanta sun kasance kanana. Ta kasance yar tsurut, lamarin da yasa mutane mamakin yadda take daukar yaron.

Mai bukata ta musamman ta santalo kyakkyawan jinjiri

Kara karanta wannan

Bayan Shekara 7 Suna Soyayya, Budurwa Ta Yi Wuff Da Dan Ajinsu, Hotunan Bikinsu Sun Kayatar

Sai dai kuma alamu sun nuna ta takura sosai a bidiyon da take zaune kan wata kujera. A wani bidiyon kuma, an ganota dauke da murmushi a fuskarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matar ta nunawa mabiyanta dan nata domin sanar da su labarin mai dadi.

Mahaifiyar, Nikki Kademaunga, ta wallafa bidiyon a shafinta na TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da mai bukata ta musamman ta santalo jinjirinta

@mutune ya ce:

"Ya yi kama da mahaifinsa."

@user702888410676 ta yi martani:

"Ina matukar alfahari da tayaki murna."

@obaapa ta yi martani:

"Na taya ki murna Kin ga ni'imar Ubangiji."

@user1691408880008 ta yi martani:

"Na tayaki murna yar'uwata."

@zhynarb ta ce:

"Na taya ki murna. Lallai Allah mai abin al'ajabi ne."

@Ashie ta yi martani:

"Allah ya sake yin mu'ujizarsa. Na tayaki murna yar'uwa."

Kara karanta wannan

“’Ya’ya Maza Nake Haifa Ba Mata Ba”: Matar Aure Ta Yi Tinkaho a Bidiyo Yayin da Ta Je Ganin Filayen Mijinta

@user3363494724759 ya ce:

"Ya yi kyau. Allah ya kasance tare da ke."

@Simone Fernandes ta yi martani:

"Wow! Na taya ki murna. Yaronki yana da kyau Allah ya ci gaba da yi maki albarka da iyalinki."

"Maza nake haifa ba mata ba", Matar aure ta yi tinkaho a bidiyo

A wani labarin, wata mata yar Najeriya mai suna @trinanicholas a TikTok ta sha caccaka a dandalin na soshiyal midiya saboda wani wallafa da ta yi a baya-bayan nan.

A cikin bidiyon, matar ta nuna farin cikinta a kan haihuwar 'ya'ya maza zalla da take yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel