Mai Neman Shugaban Kasa Ya Kyale Takara, Ya Dawo Goyon Bayan Tazarcen Tinubu
- Kennedy Ahanotu, wanda ya yi ikirarin kasancewa ɗan takarar shugaban ƙasa a tsagin jam’iyyar LP ya janye takararsa
- Yanzu yana tare da jam’iyyar APC kuma ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Bola Ahmed Tinubu a takarar 2027
- Sai dai jam’iyyar LP ta yi watsi da batun, tana mai cewa ba shi aka ba takara ba kuma an kore shi daga jam’iyyar tun tuni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Kennedy Ahanotu, wanda ya fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin wani tsagi na jam’iyyar LP ya tsallaka zuwa layin APC mai-ci.
Kennedy Ahanotu ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027 kuma ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Litinin, Ahanotu ya ce zai haɗa kai da 'yan City Boy Movement in ji jaridar The Cable.
‘Dan siyasar ya rabu da burinsa, yanzu zai wayar da kan jama’a su goyi bayan sake zaɓen Tinubu.
Kennedy Ahanotu yana goyon bayan Bola Tinubu
Ahanotu ya bayyana cewa matakin nasa ya biyo bayan ganawa da shugabannin matasan jam’iyyar LP daga jihohin Najeriya daban-daban da ya yi.
Yake cewa matasan ne suka buƙace shi da ya haɗa kai da ƙungiyar domin mara wa tazarcen Tinubu baya.
Mista Ahanotu ya danganta janyewar tasa da rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar jam’iyyar LP musamman tun bayan takarar shekarar 2023.
Punch ta rahoto shi ranar Talata yana cewa babu wanda yake farin ciki da yadda jam’iyyar ta koma, bayan shafe shekaru tana fama da rikice-rikice.
Dangantakar Ahanotu da Seyi Tinubu
Ya kuma bayyana cewa yana da kyakkyawar alaƙa da Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, tun daga shekarar 2022, kuma har ya fara hango nasara.
Matashin ya ce ya shafe shekaru 10 a jam’iyyar LP tun bayan komawa cikinta a 2016, sannan ya yi kamfen sosai domin ganin Peter Obi ya lashe zaɓe.
Da ya canza gidan a yanzu, ya zargi wasu ’yan siyasa da suka shigo jam’iyyar LP kafin zaɓen 2023 da mayar da tsofaffin mambobi saniyar ware.
Matsayar Jam’iyyar LP kan batun 'dan takarar'
Sai dai jam’iyyar LP ta yi watsi da ikirarin Ahanotu na cewa shi ɗan jam’iyyar ne ko kuma ma ɗan takarar shugaban ƙasarta a shekara mai zuwa.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ken Asogwa, ya ce an kori Ahanotu daga jam’iyyar tun ranar 14 ga Maris, 2026 don haka ba ɗan ta ba ne.
Asogwa ya ce don haka ba shi da hurumin bayyana kansa a matsayin ɗan takararta kuma za a iya ɗaukar matakin shari’a kan duk masu bata sunan LP.
Ya ƙara da cewa babu rikicin da zai sa wani ya yi amfani da hakan a matsayin dalilin sauya sheƙa, suna masu goyon bayan takarar Chibuzo Okereke.
Okereke shi ne cikakken ɗan takarar shugaban ƙasa na ɓangaren jam'iyyar LP ƙarƙashin jagorancin Sanata Nenadi Usman, wanda INEC ta yarda da shi.
Wike zai kawo wa APC nasara a Abuja
Ana da labari Nyesom Wike ya yi kira ga 'yan kwamitin yakin neman zaben APC da su hana Atiku Abubakar da Peter Obi samun kuri’u a birnin Abuja.
Ministan ya bayyana haka ne a matsayin martani ga hasashen da Rotimi Amaechi ya yi na cewa Atiku Abubakar zai lashe jihohi da dama a Arewa.
Wike ya kuma soki Atiku da cewa bai kawo wa Abuja wani ci gaba ba lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa, yana mai yabon mulkin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng