Jirgin Sojoji Ya Gamu da Mummunan Hatsari, Mutane da Dama Sun Mutu
1 - tsawon mintuna
Russia - Wani jirgin sama na jigilar kayayyakin sojojin kasar Rasha ya yi haɗari a ranar Talata a yankin Kemerovo da ke Siberiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Rahotanni sun nuna cewa dukkan mutane 19 da ke cikinsa sun mutu, kamar yadda kafafen yaɗa labaran Rasha suka ruwaito bisa bayanin ma’aikatar tsaron ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnati na TASS ya ruwaito ma’aikatar tsaron Rasha na cewa jirgin kirar An-12 ya yi haɗari ne a yankin Kemerovo yayin da yake gudanar da tafiyar da aka tsara.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng