Ebola: NCDC Ta Fadi Halin da za a Shiga a Daga Zaben 2027 a Najeriya
- Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta yi gargaɗin cewa annobar Ebola za ta iya sa a yi la’akari da jinkirta babban zaɓen 2027 idan cutar ta yaɗu sosai
- Darektan hukumar, Jide Idris, ya ce a halin yanzu babu buƙatar jinkirta zaɓen, amma jami’an lafiya na ci gaba da ganowa tare da bibiyar mutanen da ka iya kamuwa da cutar
- Ministan Lafiya ya ce ranar 7 ga Disamba ce ranar da ake hasashen Najeriya za ta iya ayyana ƙarshen annobar, amma hakan ya danganta da sakamakon sa ido da ƙa’idojin WHO
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa annobar cutar Ebola za ta iya haifar da jinkirta babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027 idan cutar ta yaɗu sosai.
Hukumar ta ce a halin yanzu babu buƙatar jinkirta zaɓen, amma idan cutar ta yaɗu sosai, gwamnati za ta iya yin la’akari da matakin domin kare lafiyar al’umma.

Source: Facebook
Darektan hukumar, Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
Ebola za ta iya shafar zaɓen 2027
Idris ya bayyana cewa jami’an lafiya ba sa amfani da cututtuka a matsayin makamin siyasa, yana mai fatan cewa annobar ba za ta kai matakin da zai sa a jinkirta zaɓen ba.
Ya ce:
“Mu a ɓangaren lafiya ba ma amfani da matsalolin cututtuka a matsayin makamin siyasa.
“Muna fatan ba za a jinkirta zaɓen ba, amma idan cutar ta yaɗu sosai, ana iya yin la’akari da hakan. A halin yanzu babu buƙatar ɗaukar irin wannan mataki.”
Darektan NCDC ya ƙara da cewa hukumar ta fara sa ido kan yiwuwar shigowar cutar daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) saboda zirga-zirgar mutane, jiragen sama da sauran hanyoyin shiga Najeriya.
Ya bayyana cewa duk da wannan sa ido, cutar ta shiga ƙasar, don haka ya zama wajibi a ci gaba da ɗaukar matakan kariya.
Karin bayani daga NCDC
Idris ya yi gargaɗin cewa har yanzu Najeriya ba ta fita daga haɗarin yaɗuwar Ebola ba, duk da fitar da majinyacin farko da aka tabbatar ya shigo da cutar daga ƙasashen waje.
PM News ta rahoto ya ce jami’an lafiya na ci gaba da gano mutanen da suka yi hulɗa da waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, domin tantance yiwuwar yaɗuwarta.
A cewarsa, kasancewar an fitar da majinyacin farko daga Najeriya ba yana nufin babu sauran masu ɗauke da cutar ba.

Source: Getty Images
Sai dai ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani tabbataccen mai cutar Ebola da ke ci gaba da jinya a Najeriya, bayan fitar da majinyacin farko zuwa ƙasar Switzerland.
An yi gargadi kan daga zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi watsi da duk wani yunƙuri na jinkirta zaɓen 2027 ko dakatar da kamfen saboda annobar Ebola a Najeriya.
Adebayo ya zargi gwamnatin jam’iyyar APC da ƙoƙarin amfani da matsalar lafiya domin cimma muradun siyasa, yana mai cewa ya kamata ƙasar ta iya kare lafiyar jama’a ba tare da tauye tsarin dimokuraɗiyya ba.
Da yake magana a wani liyafar cin abincin dare da majalisar yaƙin neman zaɓensa ta shirya a Abuja, Adebayo ya ce samun mutum guda da ya kamu da Ebola bai isa a bayyana cewa an samu annoba ba.
Asali: Legit.ng


