Abin Ya Zo: INEC Za Ta Fara Raba Katunan PVC ga Wadanda Suka Cancanta kafin Zaben 2027
- Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta fara rabon katunan zabe na dindindin (PVC) ga masu kada kuri’a da suka yi sabuwar rijista
- An ce rabon katunan zai bai wa wadanda suka yi rajista kwanan nan ko suka sauya wurin kada kuri’a damar samun katunansu gabanin babban zaben 2027
- Hukumar ta ce tana karfafa amfani da fasaha domin hana amfani da katunan zabe da aka sace, aka rasa ko aka samu matsala da su ba bisa ka’ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) na ci gaba da shirye-dhiryen tunkarar babban zaben 2027, wanda za a fara a ranar 16 ga watan Janairu mai zuwa.
Hukumar INEC ta bayyana cewa za ta fara rabon katunan zabe na dindindin (PVC) ga masu kada kuri’a da suka cancanta kuma suka yi rajista cikin kwanaki uku masu zuwa.

Source: Facebook
Yaushe INEC za ta fara raba PVC?
Tshar Channels tv ta ruwaito cewa INEC za ta fara raba katin PvC ne a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, 2027 a wani bangare na shirin babban zaben 2027 da ke kara gabatowa.
Shugaban hukumar zaben Najerirya na kasa, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tuntuba na musamman da manema labarai a Abuja yau Litinin, 5 ga watan Oktoba, 2026.
Ana sa ran aikin zai bai wa wadanda suka yi rajista kwanan nan, ko wadanda suka sauya wuraren kada kuri’arsu ko wadanda suka nemi sauya katunan zaben da suka lalace damar karbar katin PVC dinsu gabanin babban zaben 2027.
INEC na shirin babban zaben 2027
A cewar INEC, rabon katunan zaben na daga cikin shirye-shiryen da ake ci gaba da yi domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya da suka cancanta za su iya shiga cikin tsarin zabe kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu
Farfesa Amupitan ya ce hukumar tana karfafa amfani da fasaha domin tabbatar da cewa ba za a iya amfani da katunan zabe da aka sace, aka rasa ko aka samu matsala da su wajen yin katsalandan a tsarin zabe ba tare da izini ba.

Source: Facebook
Shugaban na INEC ya gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da kada su dagula yakin neman zabe, gangamin siyasa da sauran ayyukan jam’iyyun hamayya gabanin babban zaben 2027.
Wannan na zuwa ne yayin da INEC ta shirya babban taron menam labarai da masu ruwa, wand zai gudana a gobe Talata, 6 ga watan Oktoba, 2026.
INEC ta bude shafin daukar ma'aikata
A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta buɗe shafin neman aikin ma'aikatan wucin gadi da za su taimaka wajen gudanar da babban zaɓen 2027.
INEC ta ce shafin neman aikin zai kasance a buɗe har zuwa tsakar daren 18 ga Nuwamba 2026, inda ta buƙaci masu so su gaggauta shiga a wa'adin da aka tanada su cike.
INEC ta ce, ban da masu neman guraben aikin fasaha, galibi ana buƙatar masu neman aikin su kasance mazauna jihar da suka zaɓa yayin cike fom ɗin neman aikin.
Asali: Legit.ng
