Shugaban Kasa Ya Yi Murabus daga Mukaminsa kan Wasu Zarge Zarge

Shugaban Kasa Ya Yi Murabus daga Mukaminsa kan Wasu Zarge Zarge

  • Shugaban Mongoliya, Ukhnaagiin Khurelsukh, ya sanar da murabus dinsa bayan jam’iyyar adawa ta Democratic Party ta zarge shi da hannu a cin hanci
  • Khurelsukh ya musanta zargin, yana mai cewa ba zai bari jama’a da gwamnati suna tunanin ya aikata laifin sata ba
  • Shugaban majalisar dokokin ƙasar, Sandag Byambatsogt, ne zai karɓi ragamar ayyukan shugaban ƙasa, yayin da za a shirya zaɓe cikin watanni huɗu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Mongoliya - Shugaban kasar Mongoliya, Ukhnaagiin Khurelsukh, ya sanar da murabus dinsa a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba bayan fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma barazanar tsige shi daga jam’iyyar adawa ta ƙasar.

Sanarwar murabus ɗin ta zo ne kwana guda bayan jam’iyyar Democratic Party ta fitar da sanarwa, inda ta zarge shi da hannu a almundahana tare da buƙatar ya sauka daga mukaminsa ko kuma majalisa ta tsige shi.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya fito ya gayawa duniya wani halin Peter Obi

Shugaban kasar Mongoliya ya yi murabus
Shugaban kasar Mongoliya, Ukhnaagiin Khurelsukh na jawabi a wajen taro Hoto: Michele Tantussi
Source: Getty Images

Dalilin da ya sa shugaban ƙasar ya yi murabus

Da yake jawabi a wani taron manema labarai, Khurelsukh ya ce ana yi masa ƙazafi da zargin aikata manyan laifuffuka da bai aikata ba, cewar rahoton tashar Reuters.

Ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin mukaminsa ne domin ya dawo da mutuncinsa da kuma tabbatar da gaskiya game da zarge-zargen da ake yi masa.

Khurelsukh ya ce:

“Na yi imanin cewa abin da ya dace da adalci shi ne shugaban ƙasa ya ajiye aikinsa domin a gano gaskiya.
“Saboda haka, a hukumance ina sanar da cewa zan sauka daga wannan babban aikin shugaban ƙasar Mongoliya. Zan miƙa batun mutuncina ga hukumomin da suka dace domin su bincika, kuma zan nemi dawo da sunana mai kyau.”

Jam’iyyar adawa ta nemi a yi bincike

A ranar Litinin, jam’iyyar Democratic Party ta bayyana cewa cin hanci da rashawa ya yi ƙamari a Mongoliya, AP News ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Tsaro ko tazarcen Tinubu: Matawalle ya bayyana babban burinsa a 2027

Jam’iyyar ta buƙaci manyan jami’an gwamnati da ake dangantawa da zarge-zargen almundahana, ciki har da Khurelsukh, su ajiye mukamansu tare da fuskantar bincike.

Sai dai shugaban ƙasar ya musanta aikata wani laifi, yana mai cewa bai taɓa satar dukiyar jama’a ko ta gwamnati ba tun bayan hawansa kan karagar mulki.

“Ni mutum ne wanda bai taɓa satar dukiyar jama’a ko ta gwamnati ba a lokacin da nake shugaban ƙasa.
"Ban taɓa yin ƙarya ko sata ba. Ban taɓa yaudarar kowa ba.” In ji shi.

Rikicin siyasa ya ƙara kamari a Mongoliya

Mongoliya ta shafe watanni tana fuskantar rikice-rikicen siyasa, musamman sabani tsakanin ’yan jam’iyyar Mongolian People’s Party (MPP) mai mulki.

A watan Maris, ’yan majalisar dokokin ƙasar sun naɗa firaminista na uku cikin ƙasa da watanni 12, bayan zanga-zangar adawa da cin hanci da rashawa da aka shafe makonni ana gudanarwa.

Dubban matasa ne suka fito kan titunan babban birnin ƙasar, Ulaanbaatar, domin nuna fushinsu kan masu hannu da shuni da kuma abin da suke ganin rashin adalci ne da ya mamaye ƙasar.

Kara karanta wannan

Akwai kura: An taso Tinubu a gaba kan yunkurin kinkimo bashin N11trn

Wanda zai karɓi ragamar shugabancin ƙasar

Bisa dokokin Mongoliya, shugaban majalisar dokokin ƙasar, Sandag Byambatsogt, wanda yake cikin jam’iyyar MPP, zai karɓi ragamar ayyukan shugaban ƙasa bayan murabus ɗin Khurelsukh.

Dokokin ƙasar sun kuma tanadi cewa dole ne a shirya zaɓen shugaban ƙasa cikin watanni huɗu bayan barin mukamin da Khurelsukh ya yi.

Shugaban kasar Mongoliya ya sauka daga mukaminsa
Shugaba Ukhnaagiin Khurelsukh na jawabi a wajen taro Hoto: Michele Tantussi
Source: Getty Images

Shugaban maau rinjaye ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa Saleh Hodi, shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, ya yi murabus daga kujerarsa ta wakiltar mazabar Disina domin ya tsaya takarar zaben shugaban karamar hukumar Shira.

Saleh Hodi da ke wakiltar mazabar Disina, ya kasance dan majalisar tun bayan da aka fara zaben sa a shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng