APC Ta Fito da Abin da Mutane ba Su Fahimta ba kan Jawabin Tinubu a Taron Kamfen Kaduna
- Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maida martani yayin da aka fara ce-ce,-ku-ce kan jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya yi a taron kamfe a Kaduna
- APC ta ce halartar Shugaba Bola Tinubu a taron kaddamar da kamfen da aka yi a Kaduna kadai ya wadatar wajen cimma manufar taron
- Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce ba lallai ne shugaban ƙasar ya gabatar da dogon jawabi a wajen taron ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar APC ta kare Shugaba Bola Tinubu kan jawabin da ya gabatar a taron kaddamar da yakin neman zabenta da aka gudanar a Kaduna.
APC mai mulkin Najeriya ta bayyana cewa kasancewar mai girma Shugaban kass a wajen taron kaɗai ya isa wajen cimma manufar da aka shirya shi dominta.

Source: Facebook
A rahoton jaridar Vanguard, sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce ba lallai ne Tinubu ya gabatar da dogon jawabi a taron ba.
Ya ce babban manufarsa ita ce haɗa magoya bayan jam’iyyar wuri guda da kuma nuna godiya gare su bisa goyon bayan da suke ba shi gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Morka ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE News a ranar Talata, lokacin da aka tambaye shi ko jawabin da shugaban ƙasar ya gabatar a taron ranar Asabar bai kayatar ba.
APC ta kare jawabin Tinubu
Da yake mayar da martani, Morka ya ce abin da ake buƙata daga Tinubu shi ne ya halarci taron, ya gode wa al’ummar Kaduna bisa tarbar da suka yi masa da kuma goyon bayan da suke ba shi, sannan ya roƙi su sake zabensa.

Kara karanta wannan
Taohon shugaban APC na Kano ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga wurin kamfen Tinubu
A kalamansa:
“Abin da shugaban ƙasa yake buƙata shi ne a gan shi a wajen taron, ya gaya wa mutanen Kaduna, ‘Na gode muku bisa kyakkyawar tarbar da kuka yi mini, ina jin daɗin goyon bayanku, ina roƙonku ku sake yin hakan a 2027.’ Idan wannan ne kawai ya faɗa, to ya yi abin da ya dace.”
Morka ya ƙara da cewa taron kamfen irin wanda aka gudanar a Kaduna ba wurin tattaunawa kan manufofin gwamnati ba ne da ake buƙatar gabatar da dogayen jawabai.
Manufar shirya taron kamfe
Ya ce ko da shugaban ƙasar ya je taron ya yi rawa tare da gode wa jama’a kafin ya sauka daga kan dandamali, hakan ma ya isa wajen cimma manufar taron.
Sakataren yaɗa labaran APC ya ce waɗanda suka shirya taron ne suka fi cancanta su tantance ko an cimma nasarar da ake so.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa an shirya taron ne domin haɗa mambobin jam’iyyar, shugabanninta, magoya bayanta da sauran masu fatan alheri domin tarbar shugaban ƙasa.
APC ta dauki darasi daga zaben 2023
Kun ji cewa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta bayyana cewa ta koyi darasi da abin da ya faru da ita a zaben shugaban kasa na 2023 a jihar Legas.
A zaben shugaban kasa da ya wuce, APC tana ji tana gani Peter Obi na jam’iyyar LP ya doke Bola Ahmed Tinubu a gidansa.
Asali: Legit.ng

