"Ku Kasance cikin": Abin da Kwankwaso Ya Gayawa Magoya Baya bayan Kai Masa Hari

"Ku Kasance cikin": Abin da Kwankwaso Ya Gayawa Magoya Baya bayan Kai Masa Hari

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya buƙaci magoya bayansa a Bichi, Kano, su kasance cikin shiri tare da amfani da dabarar kwanton ɓauna ga duk wanda ya ƙalubalance su
  • Jawabin nasa ya biyo bayan zargin cewa wasu ’yan daba sun kai hari kan ayarin motocinsa da na ɗan takarar gwamnan NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo
  • Kakakin Kwankwasiyya ya ce Kwankwaso yana kira ne ga magoya bayansa su kasance cikin shiri don kare kansu daga hare-haren da ake zargin ana kai musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, kuma jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci magoya bayansa a Bichi, Jihar Kano, su kasance cikin shiri don fuskantar duk wata arangama da abokan hamayyar siyasa.

Kwankwaso ya kuma gaya musu cewa su yi amfani da dabarar kwanton ɓauna wajen tunkarar duk wanda ya yi musu barazana ko ƙalubalantar su.

Kara karanta wannan

Siyasa ta yi zafi: Kwankwasiyya ta yi martani mai zafi ga gwamnatin Abba

Kwankwaso ya yi kira ga magoya baya
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaao Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin kamfen a ƙaramar hukumar Bichi, bayan ƙungiyarsa ta yi zargin cewa wasu ’yan daba sun kai hari kan ayarin motocinsa yayin ziyarar siyasa a yankin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Abin da Kwankwaso ya faɗa wa magoya bayansa

Da yake jawabi ga taron, tsohon gwamnan na Kano ya ce:

“Ku ci gaba da kasancewa cikin shiri. Waɗannan marasa kunya ba sa sassautawa. Kullum muna gaya muku ku kasance cikin shiri, amma ku kasance a ƙasa, ku yi amfani da dabarar kwanton ɓauna domin tabbatar da cewa duk wanda ya ce ‘pim’ a gare mu a wannan ƙaramar hukumar Bichi...”

Jawabin nasa ya zo ne a lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin kai hari ga ayarin motocin Kwankwaso da na ɗan takarar gwamnan NDC a Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Zargin kai hari kan ayarin motocin NDC

Kakakin ɗan takarar gwamnan NDC, Ibrahim Garba Shu’aibu, ya yi zargin cewa wasu ’yan daba sun kai hari kan ayarin motocin tawagar bayan sun wuce sakatariyar ƙaramar hukumar Bichi.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima: Hadimin Tinubu ya yi babban zargi kan Kwankwaso

Ya ce harin ya jikkata wasu mambobin tawagar kamfen ɗin, sannan maharan suka lalata motoci kusan bakwai.

Shu’aibu ya bayyana cewa tawagar ta riga ta kai ziyara ƙananan hukumomin Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Bagwai ba tare da samun wata matsala ba, kafin zargin harin da aka ce ya faru a Bichi.

Kwankwasiyya ta yi bayanin jawabin jagoranta

Sai dai mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Dr Habeeb Mohammed Mailemo, ya yi bayanin cewa Kwankwaso yana ba magoya bayansa shawarar kasancewa cikin shiri ne don tunkarar duk wani yanayi da ka iya tasowa.

Ya ce hakan ya zama dole ne saboda hare-haren da ake zargin ana ci gaba da kai wa mambobin NDC, ciki har da wani lamari na baya-bayan nan da aka ce ya shafi tsohon gwamnan da kansa, jaridar Leadership ta kawo rahoton.

Dr Mailemo ya kuma jaddada cewa kare kai haƙƙi ne da aka amince da shi a duniya, musamman idan aka yi la’akari da yanayin da jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro suka gaza hana irin waɗannan hare-hare, kamar yadda ya yi zargi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi karyar da ta ce an shirya kan kai wa Kwankwaso hari

Kwankwaso ya aika da sako ga magoya baya
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jawabi a wajen taro Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Hadimin Tinubu ya zargi Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya yi zargi kan madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Bayo Onanuga ya zargi tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, da ƙarfafa magoya bayansa su shirya makamai gabanin babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng