2027: Bayan Gyare Gyare INEC za Ta Fitar da Sabon Jerin 'Yan Takara
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce za ta fitar da sabon jerin ’yan takarar zaɓen 2027 bayan kammala bitar bayanansu
- Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ta sake duba jerin ne domin gyara kuskuren rubuta sunaye da kuma matsalolin tsayawa takara
- Ana sa ran sabon jerin zai fayyace matsayin Sheikh Isa Ali Pantami na PDP a Gombe da Aminu Abdulsalam Gwarzo na NDC a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce za ta fitar da sabon jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027 bayan kammala bitar bayanan da ta samu.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Gombe, yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen wani taron tattaunawa da ma’aikatan hukumar na shiyyar Arewa maso Gabas.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa Amupitan ya ce an gudanar da bitar ne domin magance ƙorafe-ƙorafen da hukumar ta samu daga wasu ’yan takara da sauran masu ruwa da tsaki.
Hukumar INEC za ta fitar da 'yan takara
Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumar ta samu ƙorafe-ƙorafe kan kuskuren rubuta sunayen wasu ’yan takara da kuma batutuwan da suka shafi tsayawa takara a jam’iyyu fiye da ɗaya.
Ya ce hukumar ta ba da tsawon lokacin da doka ta tanada, wato kwana 14, domin gudanar da bitar tare da tabbatar da sahihancin bayanan ’yan takarar da za su shiga zaɓen.
Amupitan ya ce:
“Kamar yadda kuka sani, a duk lokacin da aka fitar da jerin sunaye, ana iya samun wasu kurakurai, kuma mun samu ƙorafe-ƙorafe kan kuskuren rubuta sunaye. Mun kuma samu ƙorafe-ƙorafe kan tsayawa takara a jam’iyyu fiye da ɗaya.
“Mun yanke shawarar amfani da cikakken lokaci na kwana 14. Nan ba da jimawa ba za mu bayyana sakamakon bitar, sannan a fitar da jerin sunayen.”
Ina makomar Isa Pantami da Aminu Gwarzo?
Shirin fitar da sabon jerin sunayen ya jawo hankalin masu bibiyar siyasa, musamman waɗanda ke son sanin matsayin wasu ’yan takara gabanin babban zaɓen 2027.
Ana sa ran sabon jerin zai fayyace matsayin Sheikh Isa Ali Pantami na jam’iyyar PDP a jihar Gombe, da Aminu Abdulsalam Gwarzo na jam’iyyar NDC a jihar Kano.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan matsayin waɗannan ’yan takara bayan bitar ba.

Source: UGC
Maganar daga zaben 2027
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce za a iya ɗage zaɓen 2027 idan annobar Ebola ta yaɗu sosai har hakan ya zama dole domin kare lafiyar jama’a.
Darektan hukumar, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata hira, inda ya ce matakin zai dogara ne da tsananin annobar da kuma yankunan da ta yaɗu zuwa.
Sai dai Idris ya jaddada cewa a halin yanzu babu dalilin tunanin ɗage zaɓen, yana mai fatan za a shawo kan annobar ba tare da kawo cikas ga jadawalin zaɓe ba.
Asali: Legit.ng

