An Rasa Rai bayan Rikici Ya Ɓarke tsakanin Makiyaya da Tawagar Kamfen Siyasa

An Rasa Rai bayan Rikici Ya Ɓarke tsakanin Makiyaya da Tawagar Kamfen Siyasa

  • Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata bayan rikici ya barke tsakanin makiyaya da tawagar motocin gangamin siyasa a jihar Jigawa
  • Rundunar NSCDC ta ce lamarin ya faru ne a hanyar Abunabo zuwa Jangon Fulani da ke karamar hukumar Guri
  • Rundunar ta tabbatar da cewa ana gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin da kuma wadanda ke da hannu a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa – An samu asarar rai bayan wani rikici ya barke tsakanin wasu makiyaya da tawagar motocin gangamin siyasa da ba a bayyana jam’iyyarsu ba a jihar Jigawa.

Rahotanni sun nuna cewa mutum daya ya mutu, yayin da wasu mutane biyu suka samu raunuka sakamakon arangamar da ta faru a karamar hukumar Guri.

An samu matsala tsakanin makiyaya da yan tawagar kamfen
Sufeta-janar na yan sandan Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, 2026, da misalin karfe 6:40 na yamma a hanyar Abunabo zuwa Jangon Fulani da ke gundumar Kadira, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'An jikkata mutane da dama a harin da aka kai wa Kwankwaso a Kano,' Obi

An tattaro cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da tawagar motocin yakin neman zabe ke wucewa ta yankin, inda suka yi arangama da wasu makiyaya.

NSCDC ta tabbatar da mutuwar mutum daya

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, jami’in hulda da jama’a na rundunar NSCDC ta Jigawa, Badaruddeen Tijjani, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa daga shugaban kungiyar Miyetti Allah na unguwar Musari, Wakili Haruna, wanda ya sanar da ita game da rikicin.

Tijjani ya bayyana cewa bayan samun rahoton, jami'an tsaro na hadin gwiwa sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Guri domin ba su kulawar likitoci.

Ya ce bayanai na farko sun nuna cewa mutane uku sun samu raunuka sakamakon harbin kibiyoyi a yayin arangamar.

Sai dai daya daga cikin wadanda suka jikkata, mai suna Ja'o Alh. Bura, dan shekara 25 daga garin Gaduwa, ya rasu bayan raunukan da ya samu.

Kara karanta wannan

"Yadda aka dakatar da limamin masallaci saboda ya ja Atiku Abubakar sallah"

An yi hatsaniya da makiyaya a Jigawa
Taswirar jihar Jigawa da aka samu hatsaniya tsakanin makiyaya da tawagar kamfen. Hoto: Legit.
Source: Original

NSCDC ta yi kira ga jama'a

Jami'in ya kara da cewa likita ne ya tabbatar da mutuwar marigayin, kafin daga bisani aka dauki hoton gawarsa tare da mika ta ga iyalansa domin yi masa jana'iza bisa tsarin addinin Musulunci.

Ya ce sauran wadanda suka jikkata sun samu kulawar likitoci, inda aka sallami daya daga cikinsu bayan an duba lafiyarsa.

A nasa bangaren, kwamandan NSCDC na jihar Jigawa, Kabiru Ingawa, ya nuna damuwarsa kan aukuwar lamarin tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin.

Kwamandan ya bukaci dukkan bangarorin da ke da hannu a rikicin da su kwantar da hankalinsu, su guji daukar matakin da zai iya kara dagula al'amura ko kawo barazana ga zaman lafiyar yankin.

An cakawa matashi wuka a Jigawa

A baya, an ji cewa rundunar ’yan sandan Jigawa ta kama matashi mai shekaru 20 bisa zargin kashe wani bayan takaddama kan bashin N500.

An ce wanda ake zargin ya daba wa matashin wuƙa bayan ya kasa biyan N500 da ya rage daga kuɗin wayar hannu da ya saya.

A wani lamari, ’yan sanda sun kama Abbas Ibrahim bisa zargin ƙona ɗakin ɗan uwansa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.