Ebola: Gwamanti Ta Ware Maƙudan Kuɗi domin Tallafawa Masu Ɗauke da Cutar
- Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta amince da biyan alawus ga kowane mutum da cutar ta kama
- Daraktan NCDC, Dakta Jide Idris, ya ce an gano mutane 53 da suka yi mu'amala da matar da ta kamu da Ebola a Abuja
- NCDC ta ce Najeriya na ci gaba da ɗaukar matakan dakile yaɗuwar Ebola, tare da kira ga jama'a su guji jita-jita kuma su ba jami'an lafiya haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta amince da biyan N100,000 ga kowane mutum da cutar Ebola ta shafa.
An ware kudin ne a matsayin tallafi kowane mako domin tallafa wa waɗanda aka killace ko aka keɓe saboda barkewar cutar Ebola a Abuja.

Kara karanta wannan
Ana zargin Ebola ta ci gaba da yaduwa a Najeriya, NCDC ta gano mutane 53 da suka yi mu'amala

Source: Twitter
Daraktan NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Lahadi, cewar Punch.
Dalilin daukar matakin ba da tallafin
Ya ce an ɗauki matakin ne bayan wasu waɗanda aka gano sun yi mu'amala da mai cutar sun koka game da kuɗin abinci, masauki da kula da iyalansu.
Idris ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan matakan da hukumar ke ɗauka domin dakile barkewar cutar.
Ya ce an samar da tallafin kuɗin ne domin waɗanda aka gano sun yi mu'amala da masu cutar su iya bin ƙa'idojin sa ido ba tare da fuskantar ƙarin matsin tattalin arziki ba.
Ya ce:
“Muna biyan kuɗin masaukinsu, muna biyan kuɗin abincinsu. Wasu daga cikinsu suna neman alawus domin kula da iyalansu.
“Muna ba da N100,000 ga kowane mutum a mako domin ya samu walwala da abinci, saboda sun yi korafi.”
Shugaban NCDC ya bayyana cewa ba a shirya wannan tallafi tun farko ba, amma yanayin da barkewar cutar ta haifar ya sa aka ga buƙatar hakan.

Kara karanta wannan
Bayan kama su da laifi, za a rataye jami'an tsaro 3 har lahira a Arewacin Najeriya
Idris ya ce:
“Ba a shirya wannan tun farko ba, amma wannan lamari ne na gaggawa. Za mu ci gaba da sake duba shi yayin da muke tafiya.”
Ya yi gargaɗin cewa sauran jihohi ma za su buƙaci tanadin kuɗi da kayayyakin aiki idan irin wannan yanayi ya taso, cewar Vanguard.
Ya ce:
“Wannan ba nauyin Abuja kaɗai ba ne. Abin da ya kamata mu yi wa Abuja, dole ne mu yi wa kowace jiha idan irin wannan abu ya faru.”

Source: Original
NCDC na sa ido kan mutane 53
Idris ya ce a lokacin taron manema labaran, Najeriya ta tabbatar da mutum ɗaya da ya kamu da cutar, yayin da aka gano mutane 53 da suka yi mu'amala kai tsaye da shi, waɗanda ake sa ido a kansu.
Mutanen sun haɗa da ma'aikatan lafiya, 'yan gidan mara lafiyar, ma'aikatan gida da kuma mutanen da suka taimaka wajen ɗaukar samfurin gwajin cutar daga gare ta.
Mutane sun sake kamuwa da cutar Ebola
Mun ba ku labarin cewa Hukumar NCDC mai kula da cututtuka masu yaduwa ta gano wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Najeriya.
Hukumar ta kuma gano mutane 53 da suka yi mu’amala kai tsaye da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar.
Darakta-Janar na NCDC, Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng
