2027: Sanatan Kano Ya Fadawa Tinubu Gaskiya kan Kalubalen da APC Za Ta Fuskanta a Arewa

2027: Sanatan Kano Ya Fadawa Tinubu Gaskiya kan Kalubalen da APC Za Ta Fuskanta a Arewa

  • Sanata Suleiman Kawu ya ce wahalar rayuwa da ta biyo bayan gyare-gyaren tattalin arziƙin Tinubu ta fusata mutane a Arewacin Najeriya
  • Dan Majalisar dattawan ya buƙaci APC ta sake kusantar talakawa tare da nuna tausayi ga halin da suke ciki gabanin zaɓen 2027
  • Kawu ya ce jam’iyyar na da kwanaki 60 na yin abin da ya dace domin sauya tunanin ’yan Najeriya da kuma ƙarfafa musu gwiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Sanatan APC mai neman komawa majalisar dattawa daga jihar Kano, ya amince cewa wahalar tattalin arziƙin da ta biyo bayan gyare-gyaren Shugaba Bola Tinubu ta fusata masu zaɓe a Arewacin Najeriya.

Sanata Suleiman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu kuma ɗan takarar APC a zaɓe mai zuwa, ya yi gargaɗin cewa dole ne jam’iyyar ta sake kusantar talakawa gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Yadda mai babur ya jawo hatsarin mota, ya rutsa da shugaban APC, daraktan kamfen

Kawu.
Sanata mai wakiltr Kano ta Kudu a Majalisar dattawa, Sulaiman Kawu Sumaila Hoto: Kawu Sumaila
Source: Twitter

Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Morning Show na tashar Arise Television

Ya ce ya kamata jam’iyyar ta amince da irin wahalar da ’yan Najeriya ke sha, sannan ta yi musu bayanin amfanin manufofin gwamnatin Tinubu da ake sa ran za su samu, maimakon dogaro da gangamin siyasa da nuna ƙarfi.

Sanatan ya amince cewa illolin tattalin arziƙin da gyare-gyaren suka haifar sun jefa jam’iyyar APC cikin ƙalubale, musamman wajen shawo kan masu zaɓe su goyi bayan sake zaɓen Tinubu.

Ya ce ya buƙaci shugabannin jam’iyyar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta su nuna tausayi da kulawa ga ’yan ƙasa bisa matsin rayuwa da ake ciki.

Ya kuma jaddada muhimmancin sake kusantar masu zaɓe a matakin ƙasa, tare da bayyana musu yadda ake sa ran gyare-gyaren gwamnatin za su samar da sauyi na zahiri a rayuwarsu.

Sanata Kawu ya ce:

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Abin da ya fi burge Atiku idan aka taɓa Tinubu yayin amfen

“Akwai ƙalubale a gaban mu musamman waɗanda suka shafi halin tattalin arziƙi sakamakon gyare-gyaren da Mai Girma Shugaban Ƙasa ya aiwatar.
“Na yi imanin cewa idan muka yi abin da ya dace cikin kwanaki 60, za mu sauya yadda ake kallon lamarin, tare da tabbatar wa ’yan Najeriya cewa muna da ƙarfin fuskantar ’yan adawa ko kuma kayar da su.”

Kawu ya bayar da misalin jihar Kano, inda ya ce mutane ba sa jin daɗin gwamnatin saboda wahalar da suke fuskanta.

“Mutane ba sa jin daɗi saboda wahalar da suke sha,” in ji shi, yana mai cewa wajibi ne jam’iyyar ta bayyana yadda gyare-gyaren za su inganta rayuwar jama’a.

Ya yi misali da tsadar kayan abinci, musamman shinkafa, a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin da gwamnati za ta iya amfani da su wajen bayyana manufofinta na tattalin arziƙi ga masu zaɓe.

Kawu ya buƙaci ’yan takarar APC da jami’an yaƙin neman zaɓen jam’iyyar su riƙa sanar da jama’a ayyukan gwamnatin a fannonin samar da ababen more rayuwa, tsaro, ilimi da kiwon lafiya, musamman ayyukan da ake gudanarwa a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262