Shugaban APC da Shugaban yakin zabe sun yi hadari a hanyar zuwa kamfe a Gombe
Gombe - An samu hadarin mota da ya shafi Shugaban APC a jihar Gombe da shugaban kwamitin yakin neman zabe na jam’iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Mohammed Dantata Ndus, da Malam Sa’adu Hassan, sun ji rauni a wannan hatsarin mota a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa taro.
Labarin da Daily Trust ta fitar ya ce sun yi hadari ne a hanyar zuwa karamar hukumar Balanga a ranar Talata 17 ga Nuwamba 2026.
Shugabanni na kan hanyarsu ne domin su haɗu da tawagar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ɗan takarar gwamnan jihar na APC.
An yi niyyar za su ci karo da su Jamil Isyaku Gwamna wajen gangamin yakin neman zaben gwamna na 2027 da aka shirya a Balanga.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana a kan hanyar Deba zuwa Talasse da ke jihar.
Wasu majiyoyi daga cikin tawagar sun ce motar ta kauce daga kan hanya ne bayan wani mai babur ya fito masu babu zato babu tsammani.
Hakan ya tilasta wa direban motar kaucewa domin gudun karo da mai babur din kai tsaye, wannan labari haka ya zo har a Premium Times.
Mista Ndus da Malam Hassan sun samu raunuka, kuma a yanzu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Gombe.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Gombe, Mista Samson Kaura, ya tabbatar wa jaridar faruwar hatsarin.
A cewar rahoton FIR na hatsarin da hukumar ta fitar, mutane bakwai ne masifar ta shafa, ciki har da wani mai babur guda ɗaya da ya rasu.
An tabbatar da cewa wannan bawan Allah ya cika a sakamakon munanan raunukan da ya samu.
Bayan haka an garzaya da mutum huɗu, ciki har da shugaban APC na jihar da daraktan yaƙin neman zaɓen, zuwa Asibitin FTH a Gombe.
Sauran mutum biyun da suka jikkata suna karɓar magani ne a Babban Asibitin Deba da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba duk a jihar Gombe.
An kuma ajiye gawar mamacin a ɗakin ajiye gawawwaki na Babban Asibitin Deba kafin a birne
Asali: Legit.ng
