Rigima Sabuwa: An Maka INEC Kara a Kotu kan Zaben 2027

Rigima Sabuwa: An Maka INEC Kara a Kotu kan Zaben 2027

  • SERAP ta bukaci INEC ta bayyana iyakar gudunmawar kudi da za a iya bai wa jam’iyyun siyasa da ‘yan takara kafin zaben 2027
  • Kungiyar ta kuma nemi INEC ta wallafa bayanan kudi, asusun da aka tantance da kuma hanyoyin samun kudaden jam’iyyun
  • SERAP ta ce yin gaskiya kan harkokin kudin siyasa na da muhimmanci domin tabbatar da sahihin tsarin zabe da damar masu kada kuri’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta kai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kotu.

Kungiyar SERAP tana zargin hukumar da kasa bayyana iyakar kudaden da za a iya bayarwa a matsayin gudunmawar siyasa gabanin babban zaben 2027.

SERAP ta kai karar INEC kara kotu
Shugaban hukumar zaben ta INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/2114/2026 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, rahoton tashar Channels tv ya nuna hakan.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a NDC kan kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso da Obi

Lauyoyin SERAP, Oluwakemi Agunbiade, Kehinde Oyewumi, Andrew Nwankwo da Valentina Adegoke ne suka shigar da karar a madadin kungiyar. Har yanzu ba a sanya ranar sauraron karar ba.

Abin da SERAP ke neman kotu ta umarta

A cikin karar, SERAP na neman kotu ta tilasta wa INEC bayyana ko ta yi amfani da ikon da aka ba ta karkashin Sashe na 91 na Dokar Zabe ta 2026 wajen kayyade iyakar kudaden gudunmawar siyasa.

Kungiyar ta kuma bukaci hukumar ta bayyana takamaiman iyakar kudaden da ta kayyade, idan har ta riga ta yi hakan, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Baya ga haka, SERAP na neman INEC ta bayyana matakan da ta tanada domin sanya ido, gudanar da bincike da kuma tabbatar da bin ka’idojin da suka shafi gudunmawar siyasa da kudaden yakin neman zabe.

SERAP ta bukaci a wallafa bayanan kudin jam’iyyu

SERAP ta kuma nemi INEC ta wallafa sababbin bayanan kudi na jam’iyyun siyasa, da suka hada da na asusu, hanyoyin samun kudade, kadarori, basussuka da kuma rahotannin kudaden da aka kashe wajen zabe daga shekarar 2023 zuwa 2025.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan soke rajistar jam'iyyar NDC

Kungiyar ta kara neman a bayyana rahotannin bincike da tantance kudaden jam’iyyun, ciki har da rahotannin da aka mika wa Majalisar Dokoki ta Kasa.

Haka kuma, ta bukaci INEC ta bayyana matakan da ta dauka kan wadanda aka samu da karya dokokin kudin siyasa.

SERAP ta ce masu kada kuri’a, ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula za su samu matsala wajen bibiyar yadda ake tafiyar da kudaden siyasa idan ba a bayyana iyakokin gudunmawa da hanyoyin sanya ido kan bin dokokin ba.

SERAP ta ce INEC bai kamata ta tsaya kawai kan karbar bayanan kudin jam’iyyun ba, domin kundin tsarin mulki ya dora mata nauyin tantance kudaden jam’iyyun da gudanar da bincike idan ya zama dole.

An kai INEC kara kotu
Taswirar birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

INEC ta sanar da dan takarar da ya yi nasara a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe zaɓen cike gurbin kujerar Dawakin Kudu/Warawa a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Dan takarar jam’iyyar, Hussaini Yusuf Datti, ya samu jimillar ƙuri’u 22,890, inda ya yi nasara a kan sauran ’yan takarar da suka fafata a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng