An Saki Sunayen Jami'an NSCDC 20 da aka Dakatar kan Mutuwar Mutum 37 a Neja
- Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja da wasu jami’ai 20 kan mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun hukumar
- Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce dakatarwar za ta ci gaba ne har sai an kammala binciken kwamitin mai zaman kansa kan lamarin
- Mun kawo jerin jami’an 20 da aka dakatar, yayin da ake ci gaba da binciken musabbabin mutuwar mutanen 37 da aka tsare bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Minna – Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya dakatar da Kwamandan rundunar NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, tare da wasu jami’ai 20 kan mutuwar mutum 37 da ke tsare a hannun hukumar.
Mutuwar mutanen ta faru ne ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026, bayan an kama wasu mutane da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Source: Facebook
Legit ta gano cewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tuji-Ojo ne ya wallafa sunayen jami'an da aka dakatar a shafinsa na X.
Ana gudanar da bincike
Punch ta wallafa cewa ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta sanar da dakatarwar ne cikin wata sanarwa da ministan ya sanya wa hannu ranar Asabar.
Gwamnatin Tarayya ta kuma kafa wani kwamiti mai mutane 10 da zai gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin.
Kwamitin zai binciki sunayen mutanen da suka mutu, yadda aka kama su da kuma yadda aka tsare su, tare da gano musabbabin da yanayin da mutuwar ta faru.
Haka kuma, an umarci kwamitin ya gano waɗanda ke da alhakin lamarin, ko akwai sakaci ko rashin bin doka, tare da bayar da shawarwari kan matakin da ya dace da kuma diyya idan ya cancanta.
Ga jerin jami’an NSCDC 20
- SC Usman Isah Ndamaka
- ASCI Hassan Mohammed
- CCA Bala Mohammed
- CSC Oluwadare Sunday
- DCC Obafemi Elvis
- CSC Annas Shitto Lamino
- DCC Philip Ajayi
- ACC Barr. Stephen Tsado
- ASCI Alhassan Mohammed
- IC Abdullahi Sale
- IC Mohammed Sonfada
- CAI Liman Abubakar CAI Bala Usman
- IC Mohammed Jiya
- DSC Isah Suleiman
- CAI Ahmed Wushishi
- IC Sale Adamu
- IC Haruna Mohammed
- ASCI Aliyu Sallah
- CAI Isah Sanusi
Mutanen 37 na daga cikin mutane da dama da jami’an NSCDC suka kama a lokacin samamen da suka gudanar a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto na Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga Satumban 2026.
Hukumar ta ce an gudanar da samamen ne domin dakile ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, inda aka kwato wasu kayayyakin da aka yi amfani da su a wuraren.

Source: Original
An hana fita a jihar Neja
A wan labarin, kun ji cewa an yi zanga-zanga a Minna bayan mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun NSCDC, inda jami’an tsaro suka yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin waɗanda suka mutu na daga cikin mutanen da aka kama yayin samamen da NSCDC ta gudanar kan ayyukan haƙar zinare da ake zargi ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin Tarayya ta umarci a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar, yayin da gwamnatin Jihar Neja da sauran hukumomin tsaro su ma suka ɗauki matakan bincike kan lamarin.
Asali: Legit.ng
