Hanyoyi 2 da Sheikh Pantami zai Bi Ya Samu Mafita a Siyasar Gombe
- Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke nasarar da Sheikh Isa Ali Pantami ya samu a matsayin ɗan takarar PDP na gwamnan jihar a zaɓen 2027
- Kotun ta umarci PDP ta gudanar da sabon zaɓen fitar gwani bayan wasu masu neman takarar gwamna sun ƙalubalanci tsarin da ya samar da Pantami
- Yayin da ake cigaba da magana kan makomar siyasar jihar Gombe, wani lauya ya ce Pantami na da zaɓi biyu a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gombe – An shiga sabon yanayi a siyasar Gombe bayan Kotun Tarayya da ke jihar ta soke nasarar Sheikh Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna na 2027.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙarar da masu neman takarar gwamna na PDP, Khamisu Mailantarki da Usman Garry, suka shigar.

Kara karanta wannan
2027: Bayan hukuncin kotu, PDP ta ɗauki matsaya kan takarar Sheikh Pantami a jihar Gombe

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa masu ƙarar sun kalubalanci tsarin da aka bi wajen bayyana Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a ranar 26 ga Yuni, 2026.
Umarnin kotu ga PDP
A hukuncin nata, Mai shari’a Amina ta ce tsarin da aka bi wajen fitar da Pantami bai cika wasu buƙatun doka da ƙa’idojin da suka dace ba.
Saboda haka, ta umarci PDP ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na gwamna bisa tsarin jam’iyyar da kuma tanadin dokokin zaɓe.
Kotun ta kuma lura cewa ba a bai wa Mailantarki da Garry damar shiga zaɓen fidda gwani na farko ba, duk da cewa an tantance su tare da amincewa da takararsu.
Pantami na da zaɓi biyu
Wani lauya daga Kano, Barrista Umar Usman Danbaito, ya ce hukuncin kotun ya yi daidai da tanadin Dokar Zaɓe ta 2026, wadda ta bai wa kotu hurumin sauraron shari’o’in da suka shafi harkokin da suka gabaci zaɓe.
Daily Trust ta rahoto cewa Danbaito ya ce Kotun Tarayya na da ikon tantance ko an samu kura-kurai wajen gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyya.
Ya ce a halin yanzu Pantami na da zaɓi biyu, ko dai ya amince da hukuncin ya shiga sabon zaɓen fidda gwani, ko kuma ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, daga bisani zuwa Kotun Ƙoli.

Source: Facebook
Batun fitar da dan takarar gwamnan Gombe
Danbaito ya ce idan mai ƙarar da ya kalubalanci takarar Pantami ya samu nasarar tabbatar da hujjojinsa, kotun ɗaukaka ƙara na iya yanke hukuncin da zai shafi wanda zai samu tikitin jam’iyyar.
Ya ce saboda haka, zai fi kyau Pantami ya bari a gudanar da sabon zaɓen fidda gwani, inda zai sake samun damar neman tikitin jam’iyyar.
Dangane da tasirin hukuncin kan babban zaɓen 2027, lauyan ya ce shari’ar ba za ta hana gudanar da zaɓen ba, saboda Dokar Zaɓe ta tanadi cewa dole a kammala dukkan shari’o’in da suka gabaci zaɓe kafin ranar babban zaɓe.
PDP za ta bi umarnin kotu
A wani labarin, kun ji cewa Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na PDP, Jungudo Haruna Mohammed, ya ce jam’iyyar za ta yi nazarin hukuncin tare da ɗaukar matakan da suka dace domin bin umarnin kotun.

Kara karanta wannan
Magana ta yi nisa, 'Tinubu Must Go' ta raba wasikun hada kan Atiku, Obi da sauransu
Ya ce PDP jam’iyya ce mai mutunta doka da hukuncin kotu, sannan za ta fara shirye-shiryen gudanar da sabon zaɓen fidda gwani a Gombe.
Shugaban PDP na Gombe, Manjo Janar Abnom Kwaskebe mai ritaya, shi ma ya ce jam’iyyar ta gamsu da hukuncin kuma za ta bi umarnin kotu wajen gyara kura-kuran da aka gano.
Asali: Legit.ng
