Shehu Buba: ‘Dan Takarar Gwamna da Ake Zargi da Ta’addanci Ya Kai Kan Shi wajen Hukuma
- Shehu Buba Umar ya mika kansa ga hukumomi domin a iya binciken zargin zargin daukar nauyin ta'addanci da ake yi masa
- ‘Dan majalisar ya bayyana cewa wadannan zarge-zarge ba sababbi ba ne, yana mai cewa ba shi da abin boyewa ko jin dar-dar
- Tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Yakubu Maikyau (SAN) ta mika takardun bincike ga hafsoshi da hukumomin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Bauchi - Shehu Buba Umar mai neman zama gwamnan jihar Bauchi a jam’iyyar PRP a 2027 ya mika kan shi gaban hukuma.
Sanata Shehu Buba Umar ya yi hakan ne domin wanke kan shi daga zarginsa da ake yi da hannu a sha’anin ta’addanci.

Source: UGC
Sanata Shehu Umar Buba ya mika kan shi
Shehu Buba Umar bayyana cewa ya mika kan shi domin jami’an DSS, DIA da ‘yan sanda su bincike shi in ji jaridar Daily Trust.
‘Dan takaran gwamnan na Bauchi yana so hukumomin tsaro su gudanar da bincike na musamman a kan zargin da ake yi masa.
Sanata Shehu Buba ya kira taron manema labarai a garin Bauchi a ranar Litinin 14 ga Satumba 2026, inda ya yi wannan jawabi.
Sanatan na Kudancin Bauchi ya ce ba yau aka fara yi masa wannan zargi ba, tun shekarar 2014 ya fara fuskantar wannan sharri.
Kalubalen da Sanata Shehu Buba ya jefa
Ya kalubalanci duk wanda yake da hujjar da ke danganta shi da ta’addanci, garkuwa da mutane ko taimakon ‘yan ta’adda ya kawo.
‘Dan majalisar ya nemi a gabatar da hujjojin kai-tsaye da jami’an tsaron da ke da alhakin gano gaskiyar wadannan tuhuma.
Ganin halin da ake ciki yau, ya ce ya zama dole ya shigo da hukuma a ciki, maimakon ya bar zancen a shafukan sada zumunta.
Tashar TVC ta rahoto shi ya ce babu wani abin da zai boye don haka ya bukaci a gudanar da bincike.

Kara karanta wannan
Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna
Shehu Buba ya dauki hayar lauyoyi
A taron manema labaran da ya yi, ya ce lauyoyinsa karkashin Yakubu Chonoko Maikyau, SAN sun aika wa hukumomi takarda.
An aika takardar zuwa Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, CDI da hafsoshin tsaro.
Yakubu Maikyau, SAN yana kuma shari’a a kotun tarayya a Abuja da wadanda ya zarga da yada labaran karya a kan shi.

Source: Facebook
Sai bayan tsawon lokaci ana zarginsa da hannu a ta’addanci sannan ya dauki wannan mataki, ya kira lamarin da sharrin siyasa.
An ji shi yana cewa da gan-gan ya ki cewa komai, yanzu din ma ya yi magana ne domin gudun a karya guiwar magoya bayansa.
Ahmad Gumi ya kare Sanata Buba
Rahoto ya zo cewa Sheikh Ahmad Gumi ya tsoma baki game da zargin alaƙa da ta'addanci da ake yi wa sanatan Jihar Bauchi, Shehu Buba.
Malamin ya bayyana cewa sanatan ya daɗe yana bai wa jami'an tsaro gudunmawa a matsayin farar hula don yaƙi da matsalar 'yan bindiga.
Gumi ya yi kira da a gudanar da bincike na adalci, sannan ya gargaɗi abokan hamayya kada su karkatar da gaskiya kan bambancin siyasa.
Asali: Legit.ng
