Karya Ta Kare: Yan Bindiga Sun Ga Bala'in da Ya Fi Karfinsu, kusan 20 Sun Bakunci Lahira
- Rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro ta kashe mutane 18 da ake zargin ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina
- Jami’an tsaro sun ƙwato bindigogin G3 da AK-47, babura da dabbobin da aka sace daga hannun yan ta'addan
- Gwamnatin Katsina ta ce za a ci gaba da farautar shugaban ƙungiyar da ya tsere a musayar wuta da jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro ta kashe ‘yan bindiga 18 a wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina.
Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Kwamishinan ma’aikatar, Dakta Nasir Mua’zu, ya fitar.

Source: Original
A cewar ma’aikatar, an gudanar da aikin ne da misalin ƙarfe 1.00 na dare ranar 21 ga Satumba a kauyen Gidan Iyado da ke yankin Kakumi, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Jami'an tsaro sun tarfa yan bindiga
Ya ce mafarauta, dakarun rundunar CWC da ‘yan sa-kai ne suka hada gwiwa suka yi wa dabar yan bindigar masu ɗauke da makamai kwanton bauna.
Ma’aikatar ta ce an gudanar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ‘yan bindigar na shirin yin garkuwa da mutane da dama domin neman kuɗin fansa a yankin.
Ma’aikatar ta bayyana ƙungiyar yan bindigar a matsayin wadda Alhaji Musa Duki ke jagoranta, wanda aka bayyana a matsayin tsohon shugaban makaranta da ake zargin ya koma fitaccen jagoran dabar ‘yan bindiga.
Dakarun tsaro sun kwato dabbobi
Sanarwar ta ce hatsabibin dan ta'addan na gudanar da ayyukansa daga Dajin Mununu da ke ƙaramar hukumar Faskari.
Jami’an tsaro sun ƙwato bindigar G3 guda ɗaya, bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 14, babura uku, shanu biyu da tumaki 94 da ake zargin ‘yan ta’addan sun sace.
Ma’aikatar tsaron Katsina ta ƙara da cewa babu wani jami’in tsaro da ya rasa ransa ko ya samu rauni a yayin arangamar.

Kara karanta wannan
Sojoji sun cafke kwamandojin 'yan ta'adda da ke da hannu a kisan babban janar a Katsina
Za a ci gaba da farautar dan ta'adda
Dr Nasir Mu'azu ya tabbatar wa mazauna yankin cewa Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayar da umarnin ci gaba da gudanar da ayyukan sirri domin gano shugaban dabar da ya tsere da kuma wargaza hanyar sadarwar laifukan ƙungiyarsa.

Source: Facebook
Kwamishinan ya yaba da jarumtar mafarauta, dakarun CWC da ‘yan banga, yana mai cewa haɗin gwiwarsu na ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro na al’umma a faɗin jihar.
Ya kuma buƙaci mazauna jihar da su tallafa wa hukumomin tsaro da sahihan bayanai cikin lokaci, yana mai jaddada cewa tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Sojoji sun kama kwamandojin yan bindiga
A wani labarin, an ji cewa Sojojin Operation Fansan Yamma tare da ’yan sa-kai sun kama wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Kachalla Maha a wani samame da aka gudanar a Katsina.
Dabar Kachalla Maha ita ce kungiyar 'yan ta'addan aka alakanta da sacewa da kashe Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya a Jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.
Asali: Legit.ng
